Shettima Ya Fadi Abin Kirki da Marigayi Sanata Ubah Ya Yi Wa Borno Lokacin Boko Haram
- Mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Kashim Shettima ya yaba da halin kirki na marigayi Sanata Ifeanyi Ubah
- Kashim Shettima ya bayyana cewa marigayin ya taɓa taimakon jihar Borno bayan wani hari da ƴan ta'addan Boko Haram suka kai
- Ya bayyana marigayin a matsayin mutumin kirki mai ƙanƙan da kai wanda yake da zuciyar taimako
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya bayyana wani halin kirki na marigayi Sanata Ifeanyi Ubah.
Kashim Shettima ya bayyana cewa marigayin ya taɓa ba da kyautar kuɗi bayan wani hari da ƴan ta'addan Boko Haram suka kai a jihar Borno.
Shettima ya faɗi halin Ifeanyi Ubah
Mataimakin shugaban ƙasan ya bayyana cewa Ifeanyi Ubah ya ba da N50m a lokacin sannan ya buƙaci ka da a gayawa duniya ya yi hakan, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shettima ya fadi hakan ne jiya Talata a wajen wani zaman bankwana da majalisar dattawa ta shirya domin karrama marigayi Sanata Ifeanyi Ubah na APC mai wakiltar Anambra ta Kudu.
Sanata Ifeanyi Ubah dai ya rasu ne a ranar 26 ga watan Yuli, 2024, yana da shekara 52 a duniya.
"Karamcinsa bai san iyaka ba. Akwai lokacin da ƴan Boko Haram suka kai hari a jihar Borno. Sanata Ifeanyi Ubah ya tuntuɓe ni."
"Ya sanya gudunmawar Naira miliyan 50 a asusuna ya ce, ‘Don Allah, ba na son a faɗi na ba da wannan gudummawar. Ifeanyi Ubah mutumin kirki ne."
- Kashim Shettima
Akpabio ya yabi Marigayi Ifeanyi Ubah
Tun da farko a nasa jawabin, shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa an ware ranar ne domin girmama rayuwar Sanata Ubah.
Akpabio ya bayyana marigayin wanda ya fito daga garin Otolo, ƙaramar hukumar Nnewi ta Arewa a jihar Anambra, a matsayin shugaba mai hangen nesa mai tausayawa kowa da kowa.
Kashim Shettima ya koka kan zanga-zanga
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana asarar da aka yi saboda zanga-zangar #EndBadGovernance.
Kashim Shettima ya ce an yi asarar sama da Naira biliyan 300 a zanga-zangar #EndBadGovernance da aka gudanar a faɗin ƙasar nan cikin watan Agusta.
Asali: Legit.ng