An Samu Asarar Rayuka bayan 'Yan Bindiga Sun Farmaki 'Yan Sanda

An Samu Asarar Rayuka bayan 'Yan Bindiga Sun Farmaki 'Yan Sanda

  • Wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci kan jami'an ƴan sanda a jihar Abia da ke yankin Kudu maso Gabas na Najeriya
  • Ƴan bindigan sun farmaki ƴan sandan ne da sanyin safiyar ranar Laraba, 20 ga watan Nuwamban 2024 a ƙaramar hukumar Ohafia ta jihar
  • Harin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan ƴan bindiga sun yi wa jami'an ƴan sanda da ke tare da wani ɗan majalisar wakilai kwanton ɓauna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Abia - Ƴan bindiga sun kashe wasu jami'an ƴan sanda da ba a tantance adadinsu ba a ƙaramar hukumar Ohafia ta jihar Abia.

Ƴan bindigan sun farmaki ƴan sandan ne da misalin ƙarfe 7:30 na safiyar yau Laraba.

'Yan bindiga sun farmaki 'yan sanda a Abia
'Yan bindiga sun kai hari kan 'yan bindiga a Abia Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Ƴan bindiga sun farmaki ƴan sanda

Jaridar The Sun ta rahoto cewa mummunan harin ya auku ne a Ebem da ke yankin Asaga na ƙaramar hukumar.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun farmaki sansanin sojoji, sun hallaka jami'ai masu yawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi sun bayyana cewa, yankin ya koma ba kowa yayin da mutane suka yi ta tururuwar guduwa domin tsira da rayukansu saboda fargaba.

Hakan na zuwa ne kwana biyu bayan ƴan bindiga sun farmaki jami’an ƴan sanda da ke tare da Hon. Ginger Onwusibe, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Isiala-Ngwa ta Arewa/Kudu a jihar Abia.

Ƴan sandan sun fuskanci harin kwanton ɓauna ne daga wajen ƴan bindigan masu dauke da makamai a lokacin da suke bakin aiki a Umuahia.

Karanta wasu labaran kan ƴan bindiga

Ƴan bindiga sun kai hari a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsagerun ƴan bindiga sun hallaka mutum biyar a kauyen Dayau da ke ƙaramar hukumar Ƙaura Namoda a jihar Zamfara da daddare.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan ɗauke da makamai sun ƙona gawarwakin waɗanda suka kashe da shaguna da rumbunan ajiyar kayayyakin abinci a ƙauyen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng