'Idan Babu Arewa, babu Najeriya,' Tinubu Ya Ce Gwamnati Za Ta Bunkasa Rayuwar Matasa

'Idan Babu Arewa, babu Najeriya,' Tinubu Ya Ce Gwamnati Za Ta Bunkasa Rayuwar Matasa

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana muhimmancin da Arewacin kasar nan ke da shi wajen bunkasa Najeriya baki dayanta
  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ne ya fadi haka a taron cigaban matasa da gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello ya shirya
  • Shugaban, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Kashim Shettima ya ce wannan ya sa ake kokarin bunkasa rayuwar matasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Najeriya ba za ta kai matakin cigaban da ake bukata ba sai an samu cigaban tattalin arzikin shiyyar Arewa.

Ya fadi haka ne a ranar Talata a wani taron cigaban matasa da gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello ta shirya a babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

"A yi mana bayanin yadda ake raba arzikin kasa," Gwamnan PDP ya taso Tinubu

Tinubu
Bola Tinubu ya jinjina muhimmancin Arewa ga Najeriya Hoto: @stanleynkwocha
Asali: Twitter

A sanarwar da hadimin mataimakin shugaban kasa, Stanley Nkwocha ya wallafa a shafinsa na X, ya ce Tinubu ya samu wakilcin Kashim Shettima a taron.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya fadi shirinsa ga matasan Arewa

Jaridar Leadership ta wallafa cewa shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta bijiro da hanyoyin ciyar da matasan kasar nan gaba ta fuskoki da dama.

Tinubu, ta bakin mataimakinsa Kashim Shettima ya kara da cewa wasu daga cikin shirye-shiryen da aka bullo da su sun hada da 3MTT na horar da matasa kan fasahar zamani.

Tinubu ya fadi muhimmancin Arewa a Najeriya

Gwamnatin tarayya ta koka bisa yadda Arewa ke da yawan yara marasa zuwa makaranta da sauran kalubale da ke bukatar kulawar gaggawa tare da amfani da yawan da ake da shi wajen bunkasa yankin.

Bola Tinubu ya ce duk abin da zai kawo nakasu ga Arewa, tamkar kawo koma baya ga kasar ne baki dayanta, wanda a cewarsa haka ta sa gwamnati ta bijiro da shirin bunkasa rayuwar matasa.

Kara karanta wannan

Bwala: An titsiye mai sukan Muslim Muslim da ya shiga gwamnatin Tinubu

Rashin tasirin manufofin gwamnatin Tinubu

A baya kun ji cewa a karon farko, Asusun bayar da lamuni na duniya (IMF) ya kalubalanci manufofin da gwamnatin Najeriya ta ce ta bijiro da su domin farfado da tattalin arziki.

Catherine Patillo, wacce ita ce mataimakiyar shugaban Asusun ta bayyana cewa manufofin ba sa aikin fitar da kasar daga wahalhalun da ta ke ciki bisa wasu matsaloli da ta lissafa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.