Kano: Yan Sanda Sun Yi Ram da Wanda Ya Zargi Kwamishinan Jigawa da Zina da Matarsa

Kano: Yan Sanda Sun Yi Ram da Wanda Ya Zargi Kwamishinan Jigawa da Zina da Matarsa

  • Rundunar yan sandan jihar Kano ta cafke mijin Tasleem Baba Nabegu bayan matarsa ta kai korafi ga kwamishinanta
  • Nasir Buba ya na tuhumar matarsa da zina da kwamishinan jihar Jigawa, Auwalu Danladi Sankara, wanda kotu ta wanke
  • Jim kadan bayan hukuncin kotun shari'ar musulunci a Kano ne yan sanda su ka bi Nasir Buba ofishin lauyansa, aka kama shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Rundunar yan sandan Kano ta cafke magidancin da ya shigar da kara gaban kotu bisa zargin kwamishinan Jigawa da zina da matarsa.

Yan sanda sun cafke Nasir Buba awanni kadan bayan babbar kotun shari'a a jihar ta wanke kwamishinan ayyuka na musamman a Jigawa, Auwalu Danladi Sankara daga zargin.

Kara karanta wannan

'Kisan mutane 17': Gwamna a Arewa ya hana Fulani daukar fansa bayan harin Lakurawa

Police
Yan sanda sun kama mijin Tasleem Baba Nabegu Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa yan sanda sun damke mijin Tasleem Baba Nabegu a ofishin lauyansa bayan daka masa ankwa jim kadan bayan ya yi watsi da hukuncin kotu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan sanda sun kama mijin Tasleem a Kano

Daily Nigerian ta ruwaito cewa yan sanda sun kama Nasir Buba jim kadan bayan ya yi fatali da hukuncin babbar kotun shari'a kan hukuncin da ta yanke.

Nasir Buba ya shaidawa manema labarai cewa ya mika hujjojinsa da su ka hada da tattaunawa ta sakon murya da bidiyo ga yan sanda kan alakar matarsa da kwamishinan Jigawa.

Kano: Dalilin yan sanda na kama mijin Tasleem

Lauyan Nasir Buba ya tabbatar da kama wanda ya ke wakilta, inda ya ce yan sanda sun kama shi ne bisa zargin binciken kwakkwafi da bibiyar matarsa ta wayar hannu.

"Yan sanda sun ce matarsa ta shigar da korafi gaban kwamishinan yan sanda, kuma ya umarci jami'an CID su gayyace shi, amma sun tafi da shi da ankwa a hannu."

Kara karanta wannan

Dubun wani ɗan sandan bogi ta cika a Kano, kwamishina ya aika sakon gargadi

Tasleem Baba Nabegu ta na zargin mijinta da yi mata kutse a waya, tare da daukar muhimman bayanai da hotuna ba tare da saninta ba.

Mijin Tasleem ya fusata da hukuncin kotu

A wani labarin kun ji cewa mijin Tasleem Baba Nabegu da ke zargin matarsa da haramtacciyar da mu'amala da kwamishinan jihar Jigawa ya yi watsi da hukuncin kotu.

Nasir Buba ya shaidawa manema labarai cewa ya yi mamaki matuka ta yadda kotu ta yi watsi da korafin da ya shigar gabanta duk da tarin hujjoji da ya mika ga rundunar yan sanda.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.