'Yan Sanda Sun Cafke Mace 'Yar Fashi da Makami da Wasu Matasa a Bauchi
- Rundunar ƴan sanda ta samu nasarar cafke wasu masu fashi da makami a jihar Bauchi da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya
- Kakakin rundunar ƴan sandan na jihar Bauchi ya bayyana cewa an cafke mutanen ne bayan samun bayanai kan ayyukan da suke aikatawa
- SP Ahmed Wakili ya sanar da cewa an ƙwato kayayyakin sata daga hannun masu fashi da makamin waɗanda a cikinsu akwai mace mai shekara 40
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bauchi - Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta cafke wata mata mai suna Maryam Salisu ƴar shekara 40 tare da wasu matasa huɗu bisa laifin fashi da makami.
Matasan da ake zargin suna fashi da makamin su ne Musa Umar, mai shekaru 17, Ibrahim Mohammed mai shekaru 17, Bilal Musa mai shekaru 17 da Idris Jibrin mai shekaru 17.
Dubun ƴan fashi da makami ta cika a Bauchi
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Wakil ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Talata a Bauchi, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce an kama waɗanda ake zargin ne biyo bayan bayanan da aka samu game da zarginsu da hannu wajen aikata laifuka.
"A yayin samamen ƴan sanda sun ƙwato kayayyakin da aka sace da suka haɗa da kwamfuta guda biyu, wayoyin hannu huɗu, caja uku, fitulu biyu, kwalaben manja guda uku, abin caji da na’urar MP3."
- Ahmed Wakil.
Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka?
SP Ahmed Wakili ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakkun ayyukan da suke yi da alaƙarsu da wasu ƙungiyoyin masu aikata laifuka, rahoton The Punch ya tabbatar.
Ya kuma ƙara da cewa rundunar a shirye take wajen tabbatar da cewa an yi gaskiya da adalci ga kowa.
Ƴan sanda sun cafke ƴan fashi da makami
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar yan sanda reshen Jigawa ta samu nasarar cafke wasu daga cikin mugayen yan fashi da makami da su ka addabi mutane.
Rundunar yan sandan jihar ta bayyana cewa ƴan fashi da makamin sun ware wasu yankuna inda su ka fi kai wa farmaki suna takurawa jama'a.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng