Gwamna Inuwa Ya Gabatar da Kasafin N320bn, An Gano Inda Zai fi Kashe Kudi a 2025

Gwamna Inuwa Ya Gabatar da Kasafin N320bn, An Gano Inda Zai fi Kashe Kudi a 2025

  • Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya gabatar da N320.11bn a matsayin kasafin kudin jihar na 2025
  • Bangaren ayyuka da gine-gine ya samu N85.219bn, wanda ya zama kaso mafi tsoka, yayin da bangaren noma ya samu 3.9%
  • Shugaban majalisa ya tabbatarwa gwamnan cewa za a duba kasafin kuɗin cikin sauri domin amfaninsa ga al’umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya gabatar da N320.11bn a matsayin kasafin kudin 2025 ga majalisar dokokin jihar.

An ce gwamnan ya gabatar da kasafin ne a ranar Talata, 19 ga watan Nuwambar 2024 inda ya zayyana bangarorin da za su fi samun kaso daga kasafin.

Gwamna Inuwa Yahaya ya gabatar da kasafin 2025 na jihar Gombe
Gwamna Inuwa zai kashe kaso 3.9 na kasafin 2025 na jihar Gombe a harkar noma. Hoto: @governor_gombe
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Gombe, jiha ce ta noma, inda tattalin arzikinta ya dogara ne kan noma amma duk da hakan iya kaso 3.9 ne kawai bangaren ya samu.

Kara karanta wannan

Tinubu zai karbo sabon bashin Naira tiriliyan 1.7, ya fadawa majalisa dalilinsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanin kasafin 2025 na jihar Gombe

Bangaren noma, wanda ke da matuƙar muhimmanci ga tattalin arzikin Gombe, ya samu N12.751bn kamar yadda rahoton ya nuna.

Rahoton ya ce an ware N32.359bn (kashi 10.1) ga ilimi daga matakin farko, yayin da bangaren manyan makarantu ya samu N15.157bn, wanda ya kai kashi 4.7.

Ma’aikatar ruwa, muhalli, da albarkatun daji ta samu N19bn, wanda ya kai kashi 5.9 na jimillar kasafin kudin 2025 na jihar da gwamnan ya gabatar.

Gwamna Yahaya ya bayyana cewa bangaren kiwon lafiya ya samu N32.418bn, wanda ya kai kashi 10.1% na jimillar kasafin kudin shekarar.

Gombe: Bangarorin da suka fi samun kaso

Bangaren ayyuka da gine-gine ne ya samu mafi yawan kaso da N85.219bn, wanda ya kai kashi 26.6% na kasafin kuɗin.

Gwamna Inuwa Yahaya ya ware kashi 34.7 (N111bn) na kasafin 2025 ga kuɗaɗen yau da kullum yayin da ya ware kashi 65.3 (N209bn) kuma ga ayyukan raya kasa.

Kara karanta wannan

Injiniya ya nuna shakku kan dalilin yawan lalacewar layin wutar lantarki

Gwamna Yahaya ya bayyana cewa kasafin zai samu tallafi daga kuɗaɗen shiga na yau da kullum na N160bn da kuma tallafin kuɗaɗen gini na N71.5bn.

Majalisa ta yabawa gwamna kan kasafin

Gwamnan ya jaddada muhimmancin duba kasafin a majalisa domin inganta shi tare da tabbatar da cewa ya amfani al’ummar jihar.

Shugaban majalisa, Abubakar Mohammed Luggerewo, ya tabbatar wa gwamnan cewa za a amince da kasafin kudin cikin kankanin lokaci domin amfanin jama’a.

Ya yaba wa Gwamna Yahaya bisa aiwatar da shirye-shiryen da suka amfani jama’a, yana mai tabbatar da cewa za a duba kasafin yadda ya kamata.

Kano: Abba ya gabatar da kasafin 2025

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bukaci majalisar Kano da ta amince da N549bn a matsayin kasafin kudin jihar na 2025.

Bangaren ilimi ya samu kaso mafi tsoka inda aka ware masa N168.5bn wanda ya kai kashi 31 yayin da bangaren kiwon lafiya ya kwashi kaso 16 (N90bn) na kasafin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.