An Shiga Fargaba bayan 'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Farmaki Jami'an NSCDC

An Shiga Fargaba bayan 'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Farmaki Jami'an NSCDC

  • Ƴan ta'addan Boko Haram sun kai hari kan jami'an tsaro na hukumar NSCDC a wani harin kwanton ɓauna a jihar Kaduna
  • Jami'an na hukumar NSCDC dai na yin aikin kula da turakun wutar lantarki a ƙaramar hukumar Shiroro lokacin da aka kai musu harin
  • Kakakin hukumar NSCDC ya bayyana cewa jami'an hukumar guda bakwai sun ɓace sakamakon harin da ƴan ta'addan suka kai musu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Ƴan ta'addan Boko Haram sun yi wa jami’an tsaro na sibil difens (NSCDC) kwanton bauna waɗanda suke kula da turakun wutar lantarki a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Ƴan ta'addan sun kai harin ne a ranar Litinin, a yankin Farin-Kasa da ke ƙaramar hukumar Chukun ta jihar Kaduna.

'Yan Boko Haram sun farmaki jami'an NSCDC a Kaduna
Jami'an NSCDC sun bace bayan harin 'yan Boko Haram a Kaduna Hoto: @OfficialNSCDC
Asali: Twitter

Boko Haram sun yi kwanton ɓauna a Kaduna

Kara karanta wannan

Zanga zanga ta ɓarke kan harbin hadimin gwamna a ofishin ƴan sanda, bayanai sun fito

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar NSCDC, Babawale Afolabi ya fitar a yammacin ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin ya bayyana cewa tawagar wacce ta ƙunshi jami’ai tara da wasu guda 71 masu muƙamai daban-daban, sun kammala aikinsu ne a Shiroro suna kan hanyar komawa sansaninsu lokacin da ƴan ta'addan suka kai musu hari.

An yi kwanton ɓaunan ne lokacin da tawagar ta raka wasu ƴan ƙasashen da aka gano a cikin dajin da ke kusa da ƙauyen Dagwachi, waɗanda ke dawowa daga wurin haƙar ma’adanai, rahoton Leadership ya tabbatar.

A cewar sanarwar, sama da mahara 200 ɗauke da muggan makamai suka far wa ayarin motocin daga saman wani tsauni, inda suka buɗe musu wuta.

Jami'an NSCDC sun daƙile harin Boko Haram

Duk da cewa an fi su yawa, jami’an na NSCDC sun yi nasarar daƙile harin, inda rahotanni suka ce sun kashe mahara fiye da 50 a yayin artabun.

Kara karanta wannan

An samu asarar rayuka bayan 'yan bindiga sun farmaki 'yan sanda

Yanzu haka dai jami’an NSCDC bakwai sun ɓace, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin gano inda suke.

Wasu kuma da dama sun samu raunuka yayin da ake duba lafiyarsu a wani asibiti.

Ƴan ta'ddan Boko Haram sun farmaki sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan ta'adda da ake zargin na Boko Haram ne sun kai farmaki kan sansanin sojoji a jihar Borno.

Harin na ƴan ta'addan ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji masu yawa tare da asarar kayan aikin jami'an tsaron masu tarin yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng