Tarin Hadimai: Tinubu Ya Kafa Tarihin Farko a Najeriya tun Mulkin Shagari a 1978
- Bola Tinubu ya zama shugaba na farko a Najeriya tun lokacin Shehu Shagari da ya fi yawan jami'ai masu magana da yawunsa
- Hakan na zuwa ne bayan da Bola Ahmed Tinubu ya nada Daniel Bwala cikin masu magana da yawansa a makon da ya wuce
- A wannan rahoton, Legit ta tattaro muku jerin shugabannin Najeriya da adadin masu magana da yawansu tun daga 1978
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A makon da ya wuce shugaba kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Daniel Bwala cikin masu magana da yawunsa.
Shugaba Bola Tinubu ya nada Daniel Bwala a matsayin mai magana da yawunsa ne bayan ya yi watsi da Atiku Abubakar.
A ranar Litinin, hadimin shugaba Bola Tinubu, Bayo Onanuga ya wallafa a Facebook cewa shugaban kasa a yanzu yana da masu magana da yawunsa guda uku.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu magana da yawun shugabannin Najeriya
1. Shehu Shagari
Shehu Shagari ya mulki Najeriya daga shekarar 1979 zuwa 1983 kuma rahoton the Cable ya nuna cewa mai magana da yawunsa shi ne:
- Charles Igoh 1979 zuwa 1983
2. Olusegun Obasanjo
Olusegun Obasanjo ya yi mulki daga 1999 zuwa 2007 kuma masu magana da yawunsa su ne:
- Doyin Okupe 1999 zuwa 2001
- Tunji Oseni 2001 zuwa 2003
- Remi Oyo 2003 zuwa 2007
Remi Oyo ce mace ta daya tilo da ta rike muƙamin magana da yawun shugaban kasa a Najeriya tun daga kan Shehu Shagari har zuwa yau.
3. Umaru Musa Yar'adua
Umaru Musa Yar'adua ya yi mulki daga 2007 zuwa 2010 kuma mai magana da yawunsa shi ne:
- Olusegun Adeniyi 2007 zuwa 2010
4. Goodluck Jonathan
Goodluck Jonathan ya jagoranci Najeriya daga 2010 zuwa 2023 kuma masu magana da yawunsa su ne:
- Ima Niboro 2010 zuwa 2011
- Rueben Abati 2011 zuwa 2015
5. Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari ya rike mulkin Najeriya daga 2015 zuwa 2023 kuma masu magana da yawunsa su ne:
- Femi Adesina 2015 zuwa 2023
- Garba Shehu 2015 zuwa 2003
6. Bola Tinubu
Bola Tinubu ya fara mukin Najeriya daga 2023 zuwa yau, kuma masu magana da yawunsa su ne:
- Ajuri Ngelale 2023 zuwa 2024
- Bayo Onanuga 2024 zuwa yau
- Sunday Dare 2024 zuwa yau
- Daniel Bwala 2024 zuwa yau
A yanzu haka Bola Tinubu yana da masu magana da yawunsa guda uku, Dare, Onanuga da Bwala inda ya zamo shugaba mafi yawan jami'ai a bangaren tun daga kan Shehu Shagari.
Bola Tinubu ya yi martani ga Obasanjo
A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta yi martani ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo kan sukar Bola Ahmed Tinubu da ya yi.
Sabon hadimin shugaba Bola Ahmed Tinubu, Sunday Dare ne ya ce Olusegun Obasanjo ba shi da hurumin sukar wata gwamnati a Najeriya.
Asali: Legit.ng