An Shiga Fargaba da Yan Sanda Suka Harbi Hadimin Gwamna, An Samu Bayanai
- Rahotanni sun tabbatar da cewa yan sanda sun karbi wani hadimin gwamnan Osun, Ademola Adeleke a Osogbo
- An ruwaito cewa yan sanda sun harbi Nuruddeen Iyanda ne bayan sun cafke shi a jiya Litinin 18 ga watan Nuwambar 2024
- Sai dai rundunar yan sanda a jihar ta yi martani inda ta ƙaryata labarin da fadin ainihin abin da ya faru
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Osun - An shiga wani irin yanayi da yan sanda a jihar Osun suka harbi hadimin Gwamna Ademola Adeleke.
Yan sanda sun karbi shugaban hukumar gudanarwar tashoshin mota a jihar, Nuruddeen Iyanda da ke kulle a wurinsu.
An harbi hadimin Gwamna Adeleke a Osun
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren hukumar, Mukaila Popoola ya fitar a yau Talata 19 ga watan Nuwambar 2024, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Popoola ya ce an harbi shugaban nasu ne da safiyar yau Talata 19 ga watan Nuwambar 2024 bayan yan sandan sun kama shi.
"An harbi shugabanmu da ke hannun yan sanda wanda ke bukatar bincike mai zurfi."
"Muna kira ga mambobinmu da su kai zuciya nesa ka da su dauki matakin doka da hannunsu, za mu tabbatar da bin dukan hanyoyin da suka dace."
- Mukaila Popoola
Yan sanda sun fadi yadda abin ya faru
Sai dai kakakin rundunar yan sanda a jihar, Emmanuel Giwa-Alade ya ce an harbi Iyanda ne lokacin da yake kokarin guduwa.
Giwa-Alade ya ce tun farko an cafke Iyanda ne a ranar Litinin da wasu mutane kan zargin yunkurin kisan kai da mallakar bindigu.
Daga bisani an tura jami'an sojoji a yankin Ilesa da ke birnin Osogbo saboda gudun tashin fitintinu, cewar The Guardian.
Jami'an sojojin sun yi wa tashar mota kawanya a yankin wanda ya yi sanadin rashin zirga-zirgan ababan hawa.
Gwamna Adeleke ya rage ranakun aiki
Kun ji cewa gwamnatin jihar Osun ta bi sahun ta jihar Ekiti wajen rage kwanakin aikin ma'aikatan jihar saboda tsadar rayuwa.
Gwamna Ademola Adeleke ne ya ce an dauki matakin ne domin saukaka halin kunci da hauhawar farashi ya jefa jama'a.
Asali: Legit.ng