An Miƙawa Gwamnatin Tinubu Buƙatar Ɗaukar Mataki kan Haihuwa Barkatai
- Wata kungiyar Association for the advancement of family planning ta roki shugaban kasa ya saki kudin tsarin iyali
- Kungiyar ta nemi haka ne a taron da ta gudanar a Abuja, inda ta ce akwai bukatar fitar da kudin bangaren na wannan shekara
- Shugaban AAFP, Dr. Ejike Oji ya ce akwai matsaloli da dama a kasar nan da yawan mutane ne ya jawo su, saboda haka a dauki mataki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Kungiyar 'Association for the Advancement of Family Planning' (AAFP) ta nemi shugaban kasa, Bola Tinubu ya cika alkawarin da ya dauka kan tsarin iyali.
AAFP ta tunatar da gwamnatin tarayya yadda ta ware zunzurutun kudi, N2bn a kasafin kudin 2024 domin sayo kayayyakin tsarin iyali.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa ana son gwamnati ta saki kudin da ta yi alkawarin bayarwa ga bangaren domin inganta tsarin tazarar haihuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An shawarci Tinubu kan tsarin iyali
Jaridar The Guardian ta tattara cewa masu ruwa da tsaki a bangaren lafiya sun taru a Abuja, inda su ka ce gwamnati na kokarin tabbatar da tsarin iyali.
Shugaban kwamitin gudanarwa na AAFP, Dr. Ejike Oji ya ce ma'aikatar lafiya ta kasa ta fitar da $4m domin sayo wasu daga cikin abubuwan da ake bukata wajen bayar da tazarar haihuwa.
Dalilin neman Tinubu ya duba tsarin iyali
Dr. Ejike Oji ya koka saboda yawan matsaloli a Najeriya, wanda ya danganta wasu daga cikinsu da yawan jama'a da ake da su a kasar.
Dr. Oji ya kara da cewa 30% na matasan kasar nan yan kasa da shekaru 34 ba su da aikin yi, ba su da ilimi kuma duk yunwa ta addabe su.
Gwamnatin Tinubu ta dauko gagarumin aiki
A baya mun ruwaito cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ce za ta fara yi wa mata masu juna biyu tiyata kyauta domin ceton rayuwar uwa da jaririn da za ta haifa.
Ministan lafiya da walwalar jama'a, Farfesa Muhammad Ali Pate ne ya bayyana fara shirin a Abuja, inda ya ce gwamnati ba ta jin dadin mace-macen mata da jariransu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng