Jerin 'Yan Kasashen Waje da Aka ba Lambobin Yabo Mafi Girma a Najeriya

Jerin 'Yan Kasashen Waje da Aka ba Lambobin Yabo Mafi Girma a Najeriya

  • An karrama firmanistan India, Narendra Modi ta lambar yabo ta biyu mafi girma a Najeriya ta 'Grand Commander of the Order of the Niger,' (GCON)
  • A 1969 an ba marigayiya Sarauniya Elizabeth II lambar yabo ta GCON, wanda hakan ya sanya Modi ya zama mutum na biyu ɗan ƙasar waje da aka ba
  • Bayan Sarauniya Elizabeth II da Narendra Modi akwai sauran ƴan ƙasashen waje da aka karrama da lambobin yabo irinsu GCFR, GCON da OFR a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - A ranar Lahadi, 17 ga watan Nuwamba, 2024, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya karrama firaministan ƙasar India, Narendra Modi.

Shugaba Tinubu ya ba Narendra Modi lambar yabo ta GCON, saboda irin rawar da ya taka da kuma irin gudunmawar da ya bayar wajen ƙulla alaƙa mai kyau tsakanin Najeriya da India.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya shilla zuwa waje bayan ganawa da shugaban kasar Indiya

'Yan kasar waje da aka ba lambar yabo a Najeriya
Narendra Modi ya shiga sahun 'yan kasashen waje da aka lambar yabo a Najeriya Hoto: Gallup/Getty Images, Thomas Imo/Photothek via Getty Images
Asali: Getty Images

Abin sani game da lambar yabo ta Najeriya

Lambobin yabo na ƙasa na Najeriya wanda aka samar ta hanyar dokar karramawa ta ƙasa mai lamba 5 ta 1964, sun kasance wani muhimmin ɓangare na tsarin karramawa a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun daga watan Oktoban 1963, ana ba da lambobin yabo duk shekara ga mutanen da suka cancanta saboda gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban ƙasa.

Ƴan kasashen waje da suka haɗa da fitattun mutane kamar Sarauniyar Ingila, Elizabeth II, Nelson Mandela, da Muammar Gaddafi, suma sun samu wannan karramawa.

Waɗannan lambobin yabon na ƙasa sun kasu daban-daban, wanda hakan ke nuna matsayinsu da muhimmancinsu.

Daga cikinsu akwai GCFR, GCON, CFR, CON, OFR, OON, MFR da MON.

Ƴan ƙasar waje da aka ba lambobin yabo

Ga cikakken jerin ƴan ƙasashen waje da aka karrama da lambobin yabo a Najeriya:

1. Sarauniya Elizabeth II - GCON

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi ruwan bama bamai kan 'yan bindiga, an sheke miyagu masu yawa

Sarauniya Elizabeth ta biyu, wacce ta fi daɗewa a kan karagar mulki a tarihin Birtaniya, an ba ta lambar yabo ta GCON a shekarar 1969.

Sannan kuma an karrama ta da lambar yabo taɓGCFR a shekarar 1989.

Kamar yadda jaridar Times of India ta ruwaito, Sarauniya Elizabeth ta biyu ita ce kaɗai ƴar ƙasar waje da ta samu wannan lambar yabo a shekarar 1969.

Sarauniyar ta rasu tana da shekaru 96 a duniya a ranar Alhamis, 8 ga watan Satumban 2022.

2. Nelson Mandela - GCFR

Marigayi Nelson Mandela, ya ziyarci Najeriya ne a shekarar 1990 domin nuna godiya bisa goyon bayan da aka ba shi a lokacin da yake tsare a gidan yari.

An shirya liyafar karrama shi ne a gidan gwamnati na Marina da ke Legas inda shugaban ƙasa, Ibrahim Babangida ya ba ba shi babbar lambar yabo ta ƙasa (GCFR), mafi girma a Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya karrama firaministan India da lambar yabo ta kasa, bidiyo ya bayyana

3. Muammar Muhammad Abu Minyar al-Gaddafi - GCFR

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, a watan Mayun 1997, Muammar Gaddafi ya ziyarci Najeriya da Jamhuriyar Nijar.

Ya samu kyautar lambar yabo ta GCFR ne a ranar 11 ga watan Mayun 1997 a Abuja daga hannun Sani Abacha, shugaban mulkin soja na lokacin.

4. Susanne Wenger - OFR

Susanne Wenger MFR, wacce aka fi sani da Adunni Olorisha, ƴar ƙasar Austria ce wacce ta dawo Najeriya.

Babban abin da ta fi mayar da hankali a kai shi ne al’adun Yarbawa kuma ta yi nasarar gina wata ƙungiya ta masu fasaha a Osogbo.

A ranar 12 ga watan Janairu, 2009, Wenger ta rasu tana da shekaru 93 a Osogbo, babban birnin jihar Osun.

Amma a shekarar 2005, gwamnatin Najeriya ta karrama Wenger ta lambar yabo ta OFR.

5. Narendra Modi - GCON

Kara karanta wannan

Dakarun sojojin sama sun samu gagarumar nasara kan 'yan bindiga

Shugaba Bola Tinubu Bola ya ba firaministan India, Narendra Modi, lambar yabo ta GCON a watan Nuwamban 2024.

Lambar yabo ta GCON da aka ba shugaba Narendra Modi, ita ce karo na 17 da aka karrama shi a ƙasashen duniya.

Shugaba Tinubu ya karrama Akpabio

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karrama shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da lambar yabo ta ƙasa.

Shugaban ƙasan ya kuma karrama alƙalin alƙalan Najeriya (CJN), Kudirat Kekere-Ekun da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Jibrin Barau.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng