Sheikh Kabiru Gombe Ya Wanke Malamai kan Halartar Liyafar Diyar Kwankwaso

Sheikh Kabiru Gombe Ya Wanke Malamai kan Halartar Liyafar Diyar Kwankwaso

  • Sheikh Kabiru Gombe ya wanke malaman addinin musulunci kan halartar diyar Rabiu Kwankwaso da dan Dahiru Mangal
  • Wannan ya biyo bayan martanin da su ka sha bayan an hango malaman a bikin 'dinner' Aisha Kwankwaso da Fahad Mangal
  • Sheikh Kabiru Gombe ya jaddada cewa alakar addini ce ta sa malaman su ka halarci liyafar ba wasu dalilai na daban ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Fitaccen Malamin addinin musulunci, Sheikh Kabiru Gombe ya fadi dalilin da ya sa malamai halartar liyafar diyar Kwankwaso da dan Dahiru Mangal.

Muhawara ta kaure tsakanin masu amfani da shafukan zumunta kan rashin dacewar malaman addinin musulunci na halartar liyafar.

Sheikh
Sheikh Kabir Gombe ya fadi dalilin zuwa liyafar diyar Kwankwaso Hoto: Karatuttukan malaman sunnah
Asali: Facebook

A bidiyon da wani mai amfani da shafin Facebook, Imam Shehu Liman ya wallafa, an ji Sheikh Kabiru Gombe ya bayyana dalilin da ya sa malaman Izala su ka ziyarci liyafar.

Kara karanta wannan

Injiniya ya nuna shakku kan dalilin yawan lalacewar layin wutar lantarki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin malamai na zuwa liyafar diyar Kwankwaso

Sheikh Kabiru Dahiru Gombe ya bayyana cewa shahararren Attajirin nan, Dahiru Mangal ya yi fice wajen taimakon addinin musulunci da dukiyarsa.

Shehin Malamin ya nanata cewa wannan na daga cikin dalilan da ya sa su ka halarci liyarfar diyar Kwankwaso da dan Dahiru Mangal a jihar Kano.

Liyafar diyar Kwankwaso: Martanin jama'a ga malamai

Jama'a sun yi martani ga kalaman Sheikh Kabiru Gombe na wanke malamai kan zuwa liyafar diyar Kwankwaso da dan Dahiru Mangal a Kano

"...Babu wanda ya san adadin masallatan juma'a da ya gina. Ban da Allah da ya halacce shi babu wanda ya san adadin makarantun Islamiyya da ya gini," cewar Malamin.

Tuni jama'a su ka fara martani kan jawabin malamin, inda wasu ke bai dace su je liyafar ba, kamar yadda wasu su ka wallafa;

Muhammad Sagir Bauchi;

"Kuma Mangal Ance, Cikakken BAQADIRE ne fa!"

Kara karanta wannan

Ganduje ya rama abin da aka yi masa, ya ki zuwa auren yar Kwankwaso a Kano

Dahiru Garba Turawa ya ce;

"To kuma duk sauran malaman a rasa waɗanda za su sai ku? Ina sauran malaman ɗariqa suke, tun da Mangal dai ba ɗan izala ba."

Ahmad Mukaddam:

"Alaƙa ce ta Addini da kuɗi ."

Malamai sun halarci liyafar diyar Kwankwaso

A baya mun wallafa cewa malaman sunnah sun halarci liyafar diyar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, Dr. A'isha da dan Attajirin nan, Dahiru Mangal, Injiniya Fahaz a Kano.

Lamarin ya ja jama'a sun rika martani ga malaman, inda ake ganin bai dace a ce malaman addini, musamman na Izala sun halarci taron da ya hada da kade-kade da raye-raye.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.