Mafi Karancin Albashi: Wike Ya Fadi Adadin Kudin da Zai Biya Ma’aikatan Abuja
- Yayin da jihohi da dama suka fara biyan mafi karancin albashi, hukumar ma'aikatan Abuja ta amince da biyan N70,000
- Ministan Abuja, Nyesom Wike shi ya tabbatar da haka domin ragewa ma'aikatan halin tsadar rayuwa da ake ciki a Najeriya
- Wannan na zuwa ne yayin da wasu jihohi suka amince da biyan fiye da N80,000 ga ma'aikatansu duba da yanayin jihohinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike ya amince zai biya mafi karancin albashi ga ma'aikatan birnin Abuja.
Wike ya amince zai biya N70,000 a matsayin mafi karancin albashi yayin da jihohi da dama suka fara biya a Najeriya.
Wike zai biya albashin akalla N70,000 a Abuja
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran hukumar ma'aikatan Abuja, Anthony Odeh ya fitar, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Odeh ya ce Wike ya amince da biyan albashin ne a ranar Litinin 18 ga watan Nuwambar 2024 domin ragewa ma'aikata halin kunci.
Sanarwar ta ce Wike ya kuma amince da biyan bashin albashin watanni uku a karshen watan Nuwambar 2024, Vanguard ta ruwaito.
Shugabar ma'aikatan Abuja na rikon kwarya, Mrs. Grace Adayilo ta tabbatar da cewa hakan na daga cikin himmatuwar Ministan wurin inganta rayuwar ma'aikata.
Ma'aikatan Abuja za su caba karkashin Wike
"Wannan mataki zai taimakawa ma'aikata domin ba da goyon baya ga Minista Wike wurin tabbatar da himmatuwar gwamnatin Bola Tinubu na inganta kasa."
- Grace Adayilo
Grace ta ce hakan na daga cikin himmatuwar gwamnatin Bola Tinubu da Wike wurin inganta rayuwar ma'aikatan Abuja.
Wike ya kori shugaban hukumar FCDA a Abuja
Kun ji cewa ministan birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya dakatar da Hadi Ahmad, shugaban hukumar raya Abuja, dakatarwa ta dindindin.
A wata sanarwa aka ya fitar a daren Alhamis, an umurci Ahmad da ya mika mulki ga daraktan sashen injiniyanci na hukumar.
An ce Wike ya yanke wannan hukunci ne saboda wasu abubuwa da ke faruwa a hukumar, kuma ya sha alwashin daidaita lamura.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng