Gwamna Ya yi Ƙarin Albashi, Ya Ɗara Yadda Tinubu ke Biyan Ma'aikata

Gwamna Ya yi Ƙarin Albashi, Ya Ɗara Yadda Tinubu ke Biyan Ma'aikata

  • Gwamnatin Benue ta sanar da ƙarin albashin ma'aikata zuwa N75,000 bayan wani zama da ta yi da kungiyar kwadago a fadin jihar
  • Gwamna Hyacinth Aliya ya bayyana dalilin zarce N70,000 da gwamnatin tarayya ta ayyana a matsayin mafi ƙarancin albashi
  • Haka zalika gwamna Alia ya yi alkawarin cigaba da yin ayyukan da za su saka ma'aikatan jihar Benue walwala da sauƙin rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Benue - Gwamnatin jihar Benue ta shiga layin sauran jihohi da suka tabbatar da karin mafi ƙarancin albashin ma'aikata.

Gwamna Hyacinth Aliya ya sanar da sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata ne a ranar Litinin, 18 ga watan Nuwamba.

Gwamna Alia
Gwamnan Benue zai fara biyan albashi N75,000. Hoto: Tersoo Kula
Asali: Twitter

Legit ta tatttaro bayanan da gwamnan ya yi ne a cikin wani sako da hadiminsa, Tersoo Kula ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Injiniya ya nuna shakku kan dalilin yawan lalacewar layin wutar lantarki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Benue: Za a biya ma'aikata N75,000

Gwamnatin jihar Benue ta sanar da sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata wanda zai fara aiki daga watan Nuwamba.

Punch ta wallafa cewa gwamna Hyacinth Aliya ya tabbatar da cewa daga watan Nuwamba sabon mafi ƙarancin albashin N75,000 zai fara aiki.

Hyacinth Aliya ya sanar da ƙarin albashin ne bayan ya gana da yan kwadago a sakatariyar jihar Benue.

"Za mu fara biyan mafi ƙarancin albashin N75,000, kuma mun yi kari a kan N70,000 ne saboda korafin da NLC ta mana.
Duk da cewa shugaba Tinubu ya ayyana N70,000 ne a matsayin mafi ƙarancin albashi, mun yi kari ne saboda muna da damar yin hakan a yanzu."

- Gwamna Hyacinth Aliya

Gwamnan ya yi alkawarin tabbatar da karin albashin a watanni uku da suka wuce kafin watan Nuwamba da a karshensa za a fara kara kudin.

Hyacinth Aliya ya kuma tabbatarwa yan kwadago cewa zai cigaba da ayyuka domin cigaban ma'aikata.

Kara karanta wannan

Ma'aikata na murna da kudi mai tsoka, Gwamna ya dakatar da biyan sabon albashi

Za a biya ma'aikata N75,000 a Kebbi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Kebbi, Nasir Idris ya amince zai biya ma'aikatan gwamnatin jihar mafi ƙarancin albashin wanda ya fi N70,000.

Mai girma gwamna Nasir Idris ya amince zai fara biya ma'aikatan jihar Kebbi sabon mafi ƙarancin albashi na N75,000 duk wata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng