Martanin Yan Arewa kan Ɗaurin Auren 'Ya'yan Sanata Barau a Fadar Aminu Ado Bayero
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ya sanar da ɗaurin auren ƴaƴansa guda biyu wanda za a yi ranar 13 ga watan Disamba, 2024.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ɗaura auren za a yi shi ne a ƙaramar fadar Nassarawa da ke cikin birnin Kano a Arewa maso Yammacin Najeriya.
Babban abin da ya fi jan hankali shi ne wurin da za a ɗaura auren wato fadar Nassarawa, inda sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ke zaune tun da aka fara rigimar sarauta.
Sanata Barau Jibrin zai aurar da ƴa ƴa 2
A katin ɗaura auren da ya wallafa a shafinsa na X, mataimakin shugaban majalisar dattawa zai aurar da ƴaƴa biyu, namiji ɗaya da mace ɗaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jibrin Barau I. Jibrin wanda zai auri ƴar gidan ɗan marigayi sarkin Kano, Ado Bayero, watau Maryam Nasir Ado Bayero.
Sai ɗan shugaban rukunin kamfanonin Azman, Injiniya Abubakar Abdulmanaf Yunus, wanda zai auri ɗiyar mataimakin shugaban majalisar dattawa, Aisha Barau I. Jibrin.
Kwankwaso ya aurar ɗiyarsa a fadar Sanusi
Wannan sanarwa na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan ɗaura auren diyar jagoran NNPP na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Manyan kusoshin gwamnatin tarayya da gwamnatin Kano, ƴan siyasa, ƴan kasuwa da sauransu sun halarci ɗaura auren Aisha Kwankwaso da Fahad Ɗahiru Mangal.
Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima na cikin waɗanda suka halarci ɗaura auren a fadar Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafin X, Kwankwaso ya nuna farin ciki da kuma godiya ga dukkan waɗanda suka halarci bikin ranar Asabar da ta gabata.
Za a ɗaura auren ƴaƴan Barau a fadar Aminu
Tun da gwamnatin Kano ta rusa masarautu biyar da Ganduje ya kirkiro tare da maido da Sanusi II kan karagar mulki, Aminu Ado ya koma fadar Nasarawa.
Rikicin sarautar Kano ya ki ci kuma ya ki cinyewa har yau, Aminu da Sanusi na ci gaba da ayyana kansu a matsayin sarakuna.
Sai dai ana zargin Sarki Aminu na samun goyon baya daga ƴan APC na Kano karkashin jagoranci Abdullahi Ganduje, wannan ya sa har yanzu ya ƙi saduda da matakin gwamnatin Kano.
Tsara ɗaura auren ƴaƴan Sanata Barau Jibrin a fadar Aminu ya ja hankalin mutane musamman waɗanda ke ganin ba shi ne halastaccen sarkin Kano ba.
Martanin ƴan Arewa kan auren ƴaƴan Barau
Legit Hausa ta zaƙulo maku wasu daga cikin kalaman da ake faɗa kan ɗaura auren ƴaƴan Sanata Barau da za a yi a fadar Nassarawa.
A I Garba (@aigarba244384) ya ce:
"Watau gidan sarki na Nasarawa, ai da ka tsaya a iya gidan sarkin kawai, ka ga inda bakin za su nufa, Allah ya ba su zaman lafiya."
Saifullahi Sagir Bala (@SaifullahiSagir) ya ce:
"Allah ya ba da zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba sanata."
Umar Abdullahi (@Umarkano_1) ya ce:
"Abin takaici ne ka kira Aminu Ado da sarkin Kano a matsayinka na jagora a majalisar ƙasa, kuna ɓata sunan Kano."
Dr. Sameera Abubakar Abdullahi ƙarin haske ta yi, inda ta ce:
"Dan Allah ka da mu masa gurguwar fahimta, katin cewa ya yi gidan sarki na Nasarawa, ba sarkin Kano na 15, Aminu Ado ba."
Jiga-jigan da suka halarci auren ɗiyar Kwankwaso
A wani rahoton, mun kawo maku yadda aka daura auren Dr Aisha Rabi'u Kwankwaso da Fahad Dahiru Mangal a jihar Kano a fadar Sanusi II.
Legit Hausa ta tattaro muku jerin jiga jigan mutane 10 a fadin Najeriya da suka halarci daurin auren ranar Asabar da ta wuce.
Asali: Legit.ng