Ministan Tinubu Ya Ba Ƴan Najeriya Tabbacin Kawo Karshen Ƴan Ta'addan Lakurawa

Ministan Tinubu Ya Ba Ƴan Najeriya Tabbacin Kawo Karshen Ƴan Ta'addan Lakurawa

  • Gwamnatin tarayya ta ɗauri ɗamar fatattakar ƴan ta'addan Lakurawa da suka fara aikata ta'addanci a Kebbi da Sakkwato
  • Ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ya ce sojoji ba za su daga ƙafa ba har sai sun ga bayan ƴan ta'addan
  • Ya faɗi haka ne yayin da ya kai ziyara domin duba wurin zama da kayan aikin rundunar Operation Fansan Yamma a jihar Sakkwato

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar ya tabbatarwa ƴan Najeriya cewa dakarun sojoji sun shirya kawo karshen ƴan ta'addan Lakurawa.

Badaru ya bukaci mutanen jihohin Kebbi da Sakkwato su kwantar da hankula, sojoji za su murƙushe ƴan Lakurawa da ƴan bindiga nan kusa.

Badaru Abubakar.
Ministan tsaro ya ce sojoji sun ɗauako hanyar kawar da ƴan ta'addan Lakurawa Hoto: Muhammd Badaru Abubakar
Asali: Facebook

Ministan ya ba da wannan tabbaci ne a jihar Sakkwato da yake rangadin duba kayan aikin rundunar sojojin sama ta Operatin Fansan Yamma, Tribune ta kawo.

Kara karanta wannan

Karshen ƴan ɓindiga ya zo, Gwamnatin Tinubu ta tura ƙarin jiragen yaƙi zuwa Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan Tiinubu ya faɗi matakin da suka ɗauka

Muhammad Badaru ya ce sojoji sun tashi tsaye, sun ɗauki tsattsauran mataki kan ƴan Lakurawa waɗanda suka fara ayyukan ta'addanci a Kebbi da Sakkwato.

Badaru ya ce:

"Kun ji daga bakin shugaban karamar hukumar da ƴan Lakurawa suka kai hari a jihar Kebbi, ya shaida tulin dakarun sojojin da muka girke.
"Tuni gwarazan jami'an tsaronmu suka fatattaki ƴan Lakurawa daga yankin gaba ɗaya. Kuna da masaniyar ruwan bama-baman da aka yi a maɓoyar ƴan bindiga.

Wane mataki sojoji suka ɗauka kan Lakurawa?

Dangane da ƴan Lakurawa, Badaru ya kara da cewa mutanen da ke zaune a yankunan da ƴan ta'addan ke kai hari su za su shaida matakin da sojoji suka ɗauka.

A cewarsa, dakarun tsaro ba za su huta ba har sai sun kakkaɓe dukkan ƴan Lakurawa da sauran kungiyoyin ƴan bindiga domin dawo da zaman ƙafiya

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun buɗewa motar jami'an tsaro wuta, sun kashe mutum 4

Ministan ya ziyarci jihar Sakkwato ne tare da rakiyar hafsan rundunar sojojin sama, Air Marshal Hasan Bala Abubakar da wasu manyan jami'ai.

Sojoji sun yi luguden wuta kan ISWAP

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin saman Nigeriya ta yi luguden wuta kan yan ta'addar ISWAP a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa sojojin saman Najeriya sun saki wuta ne a wata maboyar yan ta'addar a karamar hukumar Marte.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262