Karshen Ƴan Bindiga Ya Zo, Gwamnatin Tinubu Ta Tura Ƙarin Jiragen Yaƙi Zuwa Arewa

Karshen Ƴan Bindiga Ya Zo, Gwamnatin Tinubu Ta Tura Ƙarin Jiragen Yaƙi Zuwa Arewa

  • Ministan tsaron Najeriya, Badaru Abubakar ya jagoranci kaddamar da sababbin jiragen yaƙi samfurin ATAK-129 a jihar Katsina
  • Badaru ya ce jiragen za su taimaka wajen kawo karshen ƴan bindiga da dukkan nau'in miyagun da ke kawo cikas a zaman lafiya
  • Ya kuma jinjinawa dakarun sojoji bisa sadaukarwar da suke yi domin tabbatar zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ministan tsaro na ƙasa, Muhammad Badaru Abubakar ya ce yana da ƙwarin guiwar cewa an kusa kawo ƙarshen ƴan bindiga a Najeriya.

Badaru ya roƙi rundunar sojojin sama ta Najeriya ta haɗa kai da sauran hukumomin tsaro na ƙasa da masu ruwa da tsaki wajen kakkaɓe makiya.

Ministan tsaro a Katsina.
Ministan tsaro ya kaddamar da sababbin jiragen yaƙi masu saukar angulu a Katsina Hoto: @Jakepor21
Asali: Twitter

Gwamnatin Tinubu ta ba sojojin ƙarin jiragen yaƙi

Ministan ya yi wannan furucin ne a lokacin da ya ƙaddamar da fara aikin sababbin jiragen yaƙi samfurin ATAK-129 a Katsina, Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya ba ƴan Najeriya tabbacin kawo ƙarshen ƴan ta'addan Lakurawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Badaru tare da hafsan sojojin saman Najeriya, Air Marshal Hassan Bala Abubakar sun damka jiragen ga sashe na biyu na rundunar Opearation Fansan Yamma.

Da yake jawabi, ministan ya ce waɗannan sababbin jiragen helikwafta guda biyu sun kere sauran jiragen yaƙi kuma za su tabbatar da ba wani ɗan ta'adda da zai tsira.

"Karshen ƴan bindiga ya kusa" - Badaru

Ya ce gwamnatin ta sayo jiragen ne domin kawo karshen ƴan bindiga da duk wasu miyagu da ke kawo cikas ga zaman lafiya da ci gaban Arewa maso Yamma.

Ministan ya kuma jinjinawa dakarun sojoji bisa jajircewa da sadaukarwar da suke yi domin ceto martabar Najeriya, inda ya ce tuni kokarinsu ya fara haifar da ɗa mai ido.

Badaru ya ce abubuwa sun fara kyau, manoma sun koma gona, yara na zuwa makaranta, kasuwanci ya farfaɗo, sannan ƴan Najeriya na iya barci da ido biyu.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi ruwan bama bamai kan 'yan bindiga, an sheke miyagu masu yawa

Abubakar Badaru ya ce:

"Muna jinjina maku (sojoji) bisa sadaukarwar da kuke kan yi, kuka baro iyalai da gidajenku don ku tabbatar da martaba da ƙimar kasarmu."

Zamfara: Jiragen yaƙi sun farmaki ƴan bindiga

Kuna da labarin dakarun rundunar sojojin saman Najeriya sun samu nasarar kai hare-hare kan ƴan bindiga a jihar Zamfara

Gwarazan sojojin sun yi ruwan wuta kan ƴan bindiga a ƙauyen Babban Kauye na ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar da ke Arewa maso Yamma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262