"Mu na Barin Gidajenmu don Tsira da Rai:" Rashin Tsaro ya Addabi Mazauna Kaduna

"Mu na Barin Gidajenmu don Tsira da Rai:" Rashin Tsaro ya Addabi Mazauna Kaduna

  • Mazauna jihar Kaduna sun fara kukan neman dauki bayan yan ta'adda sun matsa da yi masu dauki dai-dai
  • Mazauna Dokan Karji a karamar hukumar Kauru da ke jihar sun bayyana cewa yan bindiga sun matsa da kai masu hari
  • Jagoran matasan yankin, Aminu Khalid a madadin mutanen yankin ya nemi babban hafsan tsaro ya kawo masu agaji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Wasu mazauna Kaduna sun bayyana cewa yan ta'adda na neman karar da su yayin da su ka matsa da hare-hare.

Mazauna Dokan Karji da ke karamar hukumar Kauru a jihar sun ce halin da su ke ciki na rashin tsaro ya zarce tunanin dan Adam.

Kaduna
Mazauna Kaduna sun nemi dauki kan rashin tsaro Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Punch ta wallafa cewa Shugaban matasan yankin, Aminu Khalid ya fitar da sanarwar neman dauki daga rundunar sojojin kasar nan.

Kara karanta wannan

'Ta burge ni': Abin da Sheikh Kabiru Gombe ya ce a liyafar auren yar Kwankwaso

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta'addanci: Mazauna Kaduna sun nemi dauki

Shugaban matasan Dokan Karji da ke jihar Kaduna, Aminu Khalid ya bukaci hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya karo masu yawan sojoji a yankin.

A sanarwar da ya fitar, Aminu Khalid ya kara da cewa yan ta'adda sun rike wuce wajen garkuwa da jama'a da kashe mutane ba tare da laifin komai ba.

Mazauna Kaduna su na gudun hijira

Wasu daga cikin mazauna jihar Kaduna, musamman na karamar hukumar Kauru sun fara barin gidajensu domin tsira da rayuwarsu.

Bayan harin da ya kashe mutane akalla 14 a baya-bayan nan, jama'a sun ce rashin tsaro ya kara kamari kuma yan bindiga na cin karensu babu babbaka.

Yan ta'adda sun harbe mafarauta a Kaduna

A wani labarin kun ji cewa wasu yan bindiga dauke da miyagun makamai sun dura a kauyen Kurutu a karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna, inda su ka tafka mummunan aiki.

Kara karanta wannan

Bello Turji da mayakansa na shan luguden wutan kwanaki 4 a jere

Yan bindigar sun kai harin kwantan bauna kauyen, inda su ka hallaka mafarauta biyu a hanyarsu ta dawowa daga daji, tare da sace wasu Fulani makiyaya daga rugarsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.