Durkusar da Arewa: Sabon Ministan Tinubu Ya Yi Wa Kwankwaso Martani, Ya Gargade Shi
- Ƙaramin ministan gidaje da raya birane ya yi martani kan kalaman da Rabiu Musa Kwankwaso ya yi na shirin durƙusar da yankin Arewa
- Yusif Abdullahi Ata ya buƙaci jagoran na jam'iyyar NNPP na ƙasa da ya guji yin kalaman da za su iya kawo tashin hankali
- Ministan ya bayyana cewa ya kamata shugabanni su riƙa tauna maganganun da za su faɗa domin gudun yin waɗanda za su iya haifar da hargitsi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kano - Ƙaramin ministan gidaje da raya birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya gargaɗi jagoran jam'iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.
Yusuf Abdullahi Ata ya buƙaci Rabiu Kwankwaso da ya guji yin kalamai waɗanda da za su iya haifar da tashin hankali.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Aminu Ibrahim, ya fitar, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Waɗanne kalamai Kwankwaso ya yi
Idan dai za a iya tunawa, Kwankwaso ya nuna damuwarsa kan cewa Shugaba Bola Tinubu na son fifita jihar Legas fiye da sauran jihohin Najeriya.
Madugun na Kwankwasiyya ya kuma yi zargin cewa yankin Legas na da hannu a rikicin masarautar Kano kuma suna shirin yi wa yankin Arewa mulkin mallaka.
Wane martani ministan ya yi wa Kwankwaso?
Sai dai, ministan ya yi gargaɗin cewa kalaman Kwankwaso na iya haifar da abin da ba a so, wanda zai iya samar da tashin hankali, rahoton Daily Post ya tabbatar.
A cewar ministan, ya kamata Kwankwaso ya tuna cewa har yanzu batun rikicin masarautar Kano na nan a gaban kotu, kuma ana iya kallon kalaman nasa na baya-bayan nan a matsayin ƙin mutunta kotu.
"A matsayinmu na shugabanni, dole ne mu ba da fifiko kan haɗin kan ƙasa da kaucewa kalaman da za su iya kawo tarzoma."
- Yusuf Abdullahi Ata
Kwankwaso ya godewa jama'a
A wani labarin kuma, kun ji cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya miƙa saƙon godiyarsa kan mutanen da suka halarci ɗaurin auren ƴarsa.
Jagoran na jam'iyyar NNPP ya ambato Shugaba Bola Tinubu a cikin saƙon nasa kan yadda ya tura Kashim Shettima domin ya wakilce shi.
Asali: Legit.ng