'Yan Bindiga Sun Buɗewa Motar Jami'an Tsaro Wuta, Sun Kashe Mutum 4
- Jami'an rundunar ƴan banga ta jihar Anambra (AVS) huɗu sun rasa rayukansu a wasu hare-hare biyu da ƴan bindiga suka kai ranar Litinin
- An ruwaito cewa ƴan bindiga da ake zaton mayakan IPOB ne sun kashe ƴan banga uku a Ukpo da mutum ɗaya a Abatete
- Kakakin ƴan sandan jihar, SP Tochukwu Ikenga ya ce jami'ai sun fara gudanar da bincien kan abin da ya faru
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Anambra - Ƴan bindiga da ake zaton ƴan kungiyar aware IPOB ne sun hallaka jami'an tsaro huɗu na rundunar ƴan banga ta Anambra (AVS) ranar Litinin.
Maharan sun kashe jami'ai AVS uku a kauyen Ukpo da ke karamar hukumar Dunukofia yayin da suka kashe wani ɗaya a Abatete, yankin Idemili ta Arewa.
Yadda ƴan bindiga suka kai hare-hare 2
Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun afka garin Abatete, inda suka yi ta harbi ba kakkautawa, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum guda.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hare-haren sun faru ne biyo bayan umarnin Gwamna Charles Soludo, wanda ya bukaci ‘yan kasuwa da su yi watsi da dokar zaman-gida a ranar Litinin.
Haramtacciyar ƙungiyar ƴan aware IPOB ce ta ƙaƙaba wannan doka ta zaman gida a kowace ranar Litinin, amma Gwamna Soludo ya umarci mutane su fita harkokin gabansu.
Ƴan bindiga sun ƙona motar AVS
Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa bayan kashe dakarun AVS guda uku a Ukpo, ‘yan bindigar sun kona motarsu ta sintiri sannan suka tsere.
Ganau ya kara da cewa ƴan bindigar na isowa shataletalen Ukpo, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi, rahoton Channels tv ya tabbatar.
A cewarsa, ana haka ne sai ga motar jami'an AVS, nan take maharan suka juya kanta da harbi, suka kashe uku daga ciki.
"Sun kawo farmaki ba zato ba tsammani, suka fara harbe-harbe suna rera 'ba ƙasar Biyafara ba ƴanci' daga nan mutane suka fara gudun neman tsira."
Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka?
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce DPO na Ukpo ya dura wurin da lamarin ya faru domin gudanar da bincike da nufin kamo waɗanda suka yi wannan aika aika.
Ƴan bindiga sun sace fasto a Anambra
A wani labarin, an ji cewa ƴan bindiga sun yi awon gaba da wani malamin coci a Awkuzu da ke ƙaramar hukumar Oyi ta jihar Anambra a shiyyar Kudu maso Gabas
Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigar sun yi awon gaba da faston a ƙofar shiga cocin ranar Asabar da ta gabata.
Asali: Legit.ng