'Yan Kasuwa Sun Buga Asara Mai Yawa yayin da Gobara Ta Babbake Wata Kasuwar Jos

'Yan Kasuwa Sun Buga Asara Mai Yawa yayin da Gobara Ta Babbake Wata Kasuwar Jos

  • Rahotanni sun bayyana cewa mummunar gobara ta tashi a kasuwar Laranto da ke Jos ta Arewa, jihar Filato a daren Lahadi
  • Shugaban kasuwar, Alhaji Idris Shehu, ya ce gobarar da ta tashi bayan an rufe kasuwar ta jawo asarar dukiyar miliyoyin Naira
  • Sai dai shugaban sashen 'yan katako na kasuwar ya koka kan yadda 'yan kwana kwanan yankin suka ki kai masu dauki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Filato - Wata mummunar gobara ta lalata dukiyar miliyoyin Naira a babbar kasuwar Laranto da ke karamar hukumar Jos ta Arewa, jihar Filato.

Rahoto ya nuna kasuwar ta dade tana fama da tashin gobara lamarin da ya dade yana ci wa 'yan kasuwar tuwo a kwarya.

Kasuwar Laranto da ke Jos ta Arewa, jihar Filato ta kama da wuta a daren ranar Lahadi
Rahoto ya ce 'yan kasuwa sun tafka asara yayin da gobara ta tashi a kasuwar Jos. Hoto: @Fedfireng
Asali: Facebook

Gobara ta tashi a kasuwar Jos

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ko a shekarar da ta gabata wata gobara ta tashi sakamakon matsalar lantarki, inda ta lalata kaya da motoci a wani bangare na kasuwar.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun gano sabon bayani kan ƴan ta'addar Lakurawa da ke addabar Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sabuwar gobarar ta faru ne da misalin karfe 11:00 na dare a ranar Lahadi, bayan an rufe kasuwar.

An ce mutanen da ke kusa da kasuwar sun yi kokarin kai dauki inda gobarar ta tashi domin kashe wutar, sai dai lamarin ya fi karfinsu.

Da yake magana kan lamarin, shugaban kasuwar, Alhaji Idris Shehu, ya bayyana cewa gobarar ta babbake kayan miliyoyin Naira, amma ba a kai ga tantance musabbabin gobarar ba.

'Yan kasuwa sun soki 'yan kwana kwana

Shugaban kasuwar ya ce wurare uku ne gobarar ta fi shafa da suka hada da bangaren 'yan katako, bangaren masu sana'ar gwanjo da bangaren masu kayan daki.

Umar Aliyu, shugaban bangaren 'yan katako, ya nuna takaici kan jinkirin isowar ma’aikatan kashe gobara, wanda ya sa lamarin ya tsananta.

“Bayan an sanar da mu game da gobarar, mun je ofishin 'yan kwana kwana na gari inda muka sanar da su. Amma jami’an suka ce ba su da mai a motocinsu.

Kara karanta wannan

Najeriya na tangal tangal, Tinubu zai runtumo sabon bashin Naira tiriliyan 4.2

"Haka gobarar ta ci gaba da ci har sai da shugaban Jos ta Arewa da kwamishinan albarkatun ruwa suka shiga maganar sannan motar kwana kwana ta gidan gwamnati ta iso wajen."

Gobara ta tashi a kasuwar Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa gobara ta lalata kusan shaguna 19 da masallaci a kasuwar Rimi, da ke karamar hukumar Kano Municipal, cikin kwaryar Kano.

Shugaban kasuwar, Alhaji Musa Tijjani Sarkin Kasuwar Rimi, wanda ya ce wutar ta tashi da tsakar dare ya ce suna zargin wutar lantarki ce ta haddasa gobarar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.