Yanzu-Yanzu: Gobarar dare ta kone shaguna kurmus a kasuwar Terminus a Jos

Yanzu-Yanzu: Gobarar dare ta kone shaguna kurmus a kasuwar Terminus a Jos

'Yan kasuwa dake da shaguna a kasuwar Terminus ta garin Jos sun tashi cikin hawaye saboda gobarar da ta kone shaguna da dama a kasuwar kamar yadda Punch ta ruwaito.

Gobarar da fara ne tun daren jiya Juma'a kuma ta kone shaguna da wuraren ajiyan kayayaki masu yawa.

A halin yanzu dai ba'a yi kiyasin dukiyar da akayi asara sakamakon gobarar ba.

A shekaran baya an taba samun tashin bam a kasuwar kuma an danganta tashin bam din da 'yan kungiyar ta'addan Boko Haram.

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar Filato, Mathias Tyopev, ya tabbatar da afkuwar gobarar a hirar da ya yi da Punch.

Yanzu-yanzu: Gobarar dare ta kone shaguna kurmus a kasuwar Terminus a Jos
Yanzu-yanzu: Gobarar dare ta kone shaguna kurmus a kasuwar Terminus a Jos

KU KARANTA: Har yanzu ina kan baka ta na ficewa daga jam'iyyar APC - Gwamna Ortom

Ya ce, "Tabbas an samu gobara a kasuwar Terminus dake Jos. Anyi asarar kayayaki kuma shaguna da dama sun kone. Kwamishinan Yan sanda na Filato, Undie Adie da Ciyaman din karamar hukumar Jos ta arewa sun ziyarci kasuwar don ganin irin abinda ya faru kuma zamu baku bayani anjima.

"A halin yanzu dai ba za mu iya kiyasin adadin dukiyar da aka rasa ba saboda akwai mutane da yawa da shagunansu ya kone; abin ya yi muni matuka saboda wutar tayi barna sosai."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164