An Shiga Tashin Hankali, Tirela Ta Murkushe Mai Karbar Haraji har Lahira a Najeriya

An Shiga Tashin Hankali, Tirela Ta Murkushe Mai Karbar Haraji har Lahira a Najeriya

  • Hukumar LASTMA ta ce wani jami'in tattara haraji a jihar Legas ya gamu da ajalisan yayin da ya ke tsallaka babbar hanyar zuwa Ibadan
  • LASTMA ta ce wani direban tirela ne ya murkushe jami'in har lahira saboda ya tsaya karbar haraji daga wajen direbobi da ke bin hanyar
  • Rundunar 'yan sandan jihar ta fara farautar direban wanda ya tsere tare da barin motarsa a kan titin bayan ganin kisan kan da ya yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Rundunar ’yan sandan jihar Legas ta fara farautar wani direban motar tirela wanda ake zargin ya murkushe mai karbar haraji har lahira.

Lamarin ya faru ne a babbar hanyar Legas zuwa Ibadan, kusa da New Garage mai shigowa Legas, inda tirelar mai lamba FST 887 XD ta murkushe jami'in.

Kara karanta wannan

Injiniya ya nuna shakku kan dalilin yawan lalacewar layin wutar lantarki

Hukumar LASTMA ta yi bayani yayin da direban tirela ya murkushe jami'in gwamnati har lahira
Legas: Direban motar tirela ya murkushe jami'in karbar haraji har lahira. Hoto: @followlastma
Asali: Twitter

Direban tirela ya murkushe jami'in LASTMA

Shugaban hukumar LASTMA, Mista Olalekan Bakare-Oki, ya ce jami'in ya gamu da ajalinsa a lokacin da ya ke kokarin karbar haraji daga direban, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bakare-Oki ya bayyana cewa direban motar ya murkushe jami'in kuma ya mutu yayin da yake ketare babbar hanyar.

Jami’an LASTMA sun hanzarta zuwa wurin da hatsarin ya faru, inda suka daidaita lamarin tare da mika gawar mamacin ga ’yan sanda.

'Yan sanda na farautar direban tirela

An mika gawar mamacin ga ofishin ’yan sanda na Adigboluje, wadanda suka tuntubi iyalansa tare da fara shirye-shiryen karbar gabawarsa.

Bakare-Oki ya nuna cewa direban da mai taimaka masa sun tsere daga wurin, lamarin da ya jawo motar da suka bari ta jawo cunkoso ababen hawa.

Rahotanni sun ce jami'an rundunar 'yan sanda sun fara farautar direban da ya yi wannan aika aika domin yanke masa hukuncin da ya yi dai dai da laifinsa.

Kara karanta wannan

‘Yan sanda sun ki karbar cin hancin Naira miliyan 174 daga hannun ‘dan damfara

Direba ya murkushe masu sharar titi

A wani labarin, mun ruwaito cewa wani direban mota ya murkushe wasu mata biyu masu sharar titi a kan hanyar Oshodi zuwa Gbagada.

An ce matan biyu sun gamu da ajalinsu ne yayin da direban ke kokarin tserewa jami'an kula da hanya ta LASTMA da ke Legas kan wani laifi da ya yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.