Kashim Shettima Ya Gyara Maganarsa bayan Ya Kira Muhammadu Sanusi II Sarkin Kano
- Kashim Shettima ya jawo hankalin jama'a bayan ya aina Malam Muhammadu Sanusi a matsayin Sarkin Kano duk da ana goyon bayan Bayero a tarayya
- Amma ya gaggauta sauya kalamansa bayan jama'a sun fara nuna jin dadin da mayar da martani kan kalaman da su ka yi hannun riga da matsayarsu
- Ana dambarwar masarautar Kano inda gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada Malam Sanusi II Sarki, gwamnatin tarayya na goyon bayan Aminu Ado Bayero
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jama’a sun fara martani kan yadda mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya kira Malam Muhammadu Sanusi II da Sarkin Kano.
Har yanzu ana dambarwa kan wanene Sarkin Kano, duk da kotu ta tabbatarwa da Malam Muhammadu Sanusi nadinsa da gwamnatin Kano ta yi.
A sakon da ya ja hankalin jama’a a shafinsa na Facebook, Kashim Shettima ya kira Malam Muhammadu Sanusi II Sarkin Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalamansa da farko sun ci karo da matsayar gwamnatin tarayya da ake zargi da goyon bayan Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin Sarki.
Kashim ya kira Sanusi sarkin Kano da farko
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya jaddada kujerar sarautar Kano ga Malam Muhammadu Sanusi II.
Ya fadi haka ne ta sakon da ya wallafa a kan halartar daurin auren diyar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da dan fitaccen dan kasuwa, Dahiru Mangal.
Daga baya sai aka ji ya sake magana, ya bayyana Sanusi II a matsayin sarki na 16, wannan ya nuna cewa ya janye matsayinsa.
Sakon Kashim ya jawo abin magana a Kano
Jama’a sun fara mayar da martani kan yadda babban kusa a gwamnatin tarayya ya kira Malam Muhammmadu Sanusi II da Sarkin Kano.
Alhassan Ali Lawan ya wallafa cewa;
“Mun ji dadin yadda aka amsa gayyata! Mun ji dadin yadda ka tabbatar da Sarkin mu a matsayin Sarkin Kano na 16. Dan takarar shugaban kasa (Rabiu Musa Kwankwason PhD) ya na maka fatan ka koma gida lafiya. Mun gode.
Yusuf Lawan ya ce;
“Toh ai sai Hamdala, na dauka ba ku aminta da Khalifa Muhammadu Sunusi II a matsayin Sarkin Kano ba ai, amma yanzu na tabbatar. Allah ya kara wa Sarki lafiya.”
Kabiru Garba ya ce;
"Al'ummar 'Headquarter' da bakin cikin Kwankwasiyya za ku mutu, kuma ko kuna so ko ba kwa so SLSII shi ne Sarkin Kano, Abba kuma shi ne gwamnan Kano."
Kashim Shettima ya halarci fadar Sarkin Kano
A baya mun ruwaito cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya halarci daurin auren diyar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da dan attajiri Dahiru Mangal a fadar Sarkin Kano.
Mataimakin shugaban kasar shi ne waliyyin ango, inda ya nemawa Injiniya Fahad Dahiru Mangal auren Dr. A'isha Rabi'u Musa Kwankwaso, tuni aka daura auren a ranar Asabar.
Asali: Legit.ng