Bola Tinubu Ya Shilla zuwa Waje bayan Ganawa da Shugaban Kasar Indiya

Bola Tinubu Ya Shilla zuwa Waje bayan Ganawa da Shugaban Kasar Indiya

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amsa gayyatar da Shugaba Luiz Inacio Lula da Silva na ƙasar Brazil ya yi masa
  • Tinubu ya shilla zuwa birnin Rio de Janeiro na ƙasar Brazil domin halartar taron ƙungiyar G20 a ranakun Litinin da Talata
  • Shugaban ƙasan ya ɗauki wata babbar tawaga ta ministocinsa wacce za ta yi masa rakiya zuwa ƙasar Brazil

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tafi birnin Rio de Janeiro na ƙasar Brazil, domin halartar taron shugabannin kasashen G20 karo na 19.

Shugaba Tinubu wanda ya bar Abuja a daren jiya bayan kammala ganawarsa da firaministan Indiya Narendra Modi, zai halarci taron ne bisa gayyatar mai masaukin baƙi, Luiz Inácio Lula da Silva.

Tinubu ya tafi Brazil
Shugaba Tinubu ya tafi kasar Brazil Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Bola Tinubu zai halarci taron G20

Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar, wacce Dada Olusegun ya sanya a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Zaben Ondo 2024: Dan takarar gwamna ya fadi rawar da Tinubu zai taka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron zai haɗa shugabanni daga manyan ƙasashen duniya masu ƙarfin tattalin arziƙi, tare da wakilai daga tarayyar Afirka, tarayyar Turai, da manyan cibiyoyin hada-hadar kuɗi na ƙasa da ƙasa.

Za a gudanar da taron ne a ranakun Litinin, 18 ga watan Nuwamba da Talata, 19 ga watan Nuwamban 2024.

A gefen taron, ana sa ran shugaba Tinubu zai gudanar da tarurruka domin ci gaba da tallata ajandar sake fasalin tattalin arziƙin Najeriya.

Su wanene ƴan rakiyar shugaba Tinubu

Tare da shugaban ƙasar akwai wata babbar tawaga da ta haɗa da ministan harkokin waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ministan kiwon dabbobi, Idi Mukhtar Maiha da ministar yawon bude ido da al'adu, Hannatu Musawa.

Sauran sun haɗa da ƙaramin ministan noma da samar da abinci, Dr. Aliyu Sabi Abdullahi da Darakta-Janar na hukumar leken asiri ta ƙasa (NIA) Ambasada Mohammed Mohammed.

Ana sa ran shugaba Tinubu zai dawo gida Najeriya bayan kammala taron.

Kara karanta wannan

Lagbaja: Shugaba Tinubu ya karrama marigayi hafsan sojojin ƙasa a wurin jana'iza

Tinubu ya taya Aiyedatiwa murna

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi magana bayan sanar da sakamakon zaben jihar Ondo a ranar Lahadi, 17 ga watan Nuwamban 2024.

Shugaba Tinubu ya taya Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jam'iyyar APCmurnar lashe zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar 16 ga watan Nuwamban 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng