Dutsen Tanshi Ya Gwabji Malamai, Ya Ragargaji Wadanda Sarkin Musulmi ya ba Sarauta

Dutsen Tanshi Ya Gwabji Malamai, Ya Ragargaji Wadanda Sarkin Musulmi ya ba Sarauta

  • Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya soki yadda ya ga malaman musulunci sun karbi sarauta
  • Malamin musuluncin bai ganin dacewar takawaransa ya rika bajewa gaban mai sarautar gargajiya
  • A ra’ayin Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, babu abin murna idan Sarki ya daurawa mutum rawani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Bauchi - An sake jin Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya yi magana a kan sarautar gargajiyar da ake ba malamai kwanan nan.

Malamin ya na ganin cewa sam bai kamata masanin addinin musulunci ya karbi wata sarauta daga wajen sarkin gargajiya ba.

Sarkin Musulmi
Sarkin Musulmi ya ba wasu malaman addini sarauta Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Idris Dutsen Tanshi ya soki karbar sarauta

A wani fai-fai da Legit Hausa ta samu a shafin Facebook, an ji Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi yana tir da karbar sarauta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fitaccen malamin da yake garin Bauchi ya fita dabam, ya ce an saba yi masa tayin irin wannan sarauta amma bai karba ba.

Kara karanta wannan

Injiniya ya nuna shakku kan dalilin yawan lalacewar layin wutar lantarki

A jawabinsa, ya ce akwai wasu wadanda suke da’awar malanta kuma sun karbi nadin sarauta daga Sarkin Musulmi a Sokoto.

“Wallahi malamin sunnah da ya san darajar ilmi, ba zai karbi sarautar gargajiya ba. An sha ba ni, na ce masa a’a.
Mukamin da na ke kai ya fi kowace sarauta. Malamai su ne magada Annabawa.”

- Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi

Matsalar sarauta a wajen Idris Dutsen Tanshi

Tsoron da yake yi shi ne idan malami zai sa rawanin basarake, za a iya rudar gama-garin al’umma su rika karbar sarauta.

Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya yi hujja da maganar Shehu Danfodio, ya ce ya hana karbar irin sarauta a karatunsa.

Akwai wani da ya taba samun sarauta, sai ya kira malamin ya taya sa murna, shi kuwa sai ya ce ai bakin ciki zai taya shi.

Shehin ya soki tsarin da cewa idan mutum ya sa rawani, zai rika fadi gaban sarki, shi kuma fadawa su rika faduwa gabansa.

Kara karanta wannan

'Ta burge ni': Abin da Sheikh Kabiru Gombe ya ce a liyafar auren yar Kwankwaso

Sarkin Musulmi ya ba malamai sarauta

Rahoto ya zo cewa Sarkin Musulmi watau Abubakar Sa'ad III ya ba tsohon minista, Farfesa Isa Ali Pantami sarauta a daular Usmaniyya.

Shi kuma babban malamin nan, Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto zai samu sarautar 'dan masani daga wajen Mai alfarma Abubakar Sa'ad.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng