'Yan Bindiga Sun Sace Babban Jami'in Hukumar NDLEA, an Samu Bayanai

'Yan Bindiga Sun Sace Babban Jami'in Hukumar NDLEA, an Samu Bayanai

  • Wasu ƴan bindiga sun yi ta'asa a jihar Delta bayan sun sace wani babban jami'in hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEA
  • Ƴan bindigan sun sace jami'in ne a kusa da ofishin hukumar a daren ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamban 2024
  • Jami'in na NDLEA dai ya faɗa hannun ƴan bindigan ne bayan sun yi masa kwanton ɓauna lokacin da yake kan hanyar komawa gida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Delta - Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da wani babban jami’in hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) a jihar Delta.

Ƴan bindigan sun sace jami'in na NDLEA ne tare da mai ba shi kariya a kusa da babban ofishin hukumar da ke kan hanyar Isah-Ogwashi-Uku a ƙaramar hukumar Aniocha ta Kudu a jihar Delta.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi ta'addanci, sun hallaka tsohon kansila har lahira

'Yan bindiga sun sace jami'in NDLEA a Delta
'Yan bindiga sun sace jami'in hukumar NDLEA a jihar Delta Hoto: @ndlea_nigeria
Asali: Facebook

Yadda ƴan bindiga suka sace jami'in NDLEA

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:00 na daren ranar Asabar a daidai lokacin da jami’in ya nufi gida bayan ya tashi daga aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ƴan bindigan sun yi musu kwanton ɓauna, inda suka tilasta musu shiga wata mota kafin su arce daga wurin.

"Alamu sun nuna cewa masu garkuwa da mutanen sun samu bayanai kan duk motsinsa. Sun shirya kwanton ɓaunan da kyau wanda hakan ya nuna sun daɗe suna bibiyarsa."

- Wata majiya

Wannan sace-sacen dai shi ne na baya-bayan nan da aka yi a garin Ogwashi-Uku, inda a cikin kwanaki 10 da suka gabata aka yi garkuwa da mutane sau biyar.

Me NDLEA ta ce kan lamarin?

Da aka tuntuɓi kakakin hukumar NDLEA reshen jihar Delta, Mista John Kennedy, ya ƙi cewa komai kan lamarin.

Kara karanta wannan

Zaben Ondo: Ana dab da fara zabe, 'yan daba sun farmaki 'yan PDP

An tattaro cewa ana ci gaba da ƙoƙarin gano jami’in da aka sace tare da mai ba shi kariya.

NDLEA ta cafke ƙwayoyi

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar NDLEA ta dakile yunƙurin fitar da miyagun kwayoyi zuwa Biritaniya ta hanyar gano su cikin buhunan gyada da aya.

Shugaban sashen harkokin yaɗa labarai na NDLEA, Femi Babafemi, ya bayyana cafke kayayyaki a cikin bidiyon da aka wallafa a shafukan sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng