Kaduna: Rundunar Tsaro Ta Magantu kan Biyan Kudin Fansar Mutane 58 da Aka Sace
- Wasu mutane 58 da aka yi garkuwa da su a Birnin Gwari sun shaki iskar yanci inda aka mika su ga gwamnatin Kaduna
- Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa shi ya tabbatar da haka inda ya ce ko sisn kwabo ba a biya ba wurin sakinsu
- Janar Musa ya bayyana rawar da Gwamna Uba Sani da Nuhu Ribadu suka yi wurin tabbatar da sakin mutanen da aka kama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Rundunar tsaro a Najeriya ta yi magana kan jita-jitar biyan kudin fansa kan mutane 58 da suka kubuta.
Rundunar ta musanta rade-radin cewa ta biya kudi inda ta ce sisin kwabonta bai yi ciwon kai ba.
Yadda aka sace mutane 58 a Kaduna
The Guardian ta ce hafsan tsaro, Janar Christopher Musa shi ya tabbatar da haka yayin mika mutanen ga gwamnatin jihar Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Janar Musa ya ce yan bindiga sun kama mutanen ne a Birnin Gwari da ke jihar Kaduna da suka hada da mata 23 da kuma maza 35 inda suka sake su a ranar 14 ga watan Nuwambar 2024.
Hafsan tsaro ya yabawa Ribadu, Uba Sani
Hafsan tsaron ya kuma yabawa Gwamna Uba Sani da mai ba Bola Tinubu shawara a harkar tsaro, Nuhu Ribadu kan rawar da suka taka.
Ya ce ko sisi ba a biya ba sai dai an saki mutanen ne bayan wata yarjejeniya da Uba Sani ya yi da hadin guiwar ofishin Nuhu Ribadu, cewar Tribune.
Bayan sakin mutanen da suka hada da mata da kuma yara an wuce da su ofishin Nuhu Ribadu domin ba su kulawar lafiya da yi musu tambayoyi.
Kaduna: Yan bndiga sun kona abincin N100m
Kun ji cewa dan majalisar wakilai daga Birnin Gwari, Hon. Zubairu Birnin Gwari ya nemi daukin gwamnatin tarayya daga 'yan ta'adda.
Hon. Zubairu Birnin Gwari ya ce mutanensa sun yi asarar akalla Naira miliyan 100 a harin da yan bindiga su ka kai Kaduna.
Dan majalisar ya na ganin lokaci ya yi da jama'a za su fara kare kawunansu daga yan ta'adda idan gwamnati ta gaza.
Asali: Legit.ng