Fitaccen Dan Daudu Ya Maka EFCC da Majalisar Tarayya a Kotu, Yana Neman N1.2bn

Fitaccen Dan Daudu Ya Maka EFCC da Majalisar Tarayya a Kotu, Yana Neman N1.2bn

  • Fitaccen dan daudu, Bobrisky ya shigar da ƙara kan EFCC da majalisar tarayya, yana zargin sun take haƙƙinsa ta hanyar tsare shi
  • Ya ce gayyatar majalisar tarayya domin bincike ya samo asali ne daga wani sautin murya da ba a tabbatar da sahihancinsa ba.
  • Bobrisky ya na neman diyyar Naira biliyan 1.2, inda ya ce abin da EFCC da majalisar suka yi masa ya jefa shi a cikin damuwa sosai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Fitaccen ɗan daudun Najeriya, Idris ‘Bobrisky’ Okuneye ya maka EFCC da majalisar tarayya gaban kotu yana zargin an ci zarafinsa da tauye masa hakki.

Bobrisky dai ya shiga cikin cakwakiya a kwanakin baya kan bullar wani sautin murya da aka ce tashi ce yana ikirarin cewa EFCC ta karbi kudinsa domin wanke shi daga tuhuma.

Kara karanta wannan

‘Yan sanda sun ki karbar cin hancin Naira miliyan 174 daga hannun ‘dan damfara

Bobrisky ya dauki mataki kan EFCC da majalisar tarayya bayan tsare shi da gayyatarsa
Dan daudu, Bobrisky ya gurfanar da EFCC da majalisar tarayya gaban kotu. Hoto: bobrisky222
Asali: Instagram

Bobrisky ya yi karar EFCC, majalisar tarayya

Premium Times ta rahoto Bobrisky ya wallafa takardar kotu da ta hana EFCC da majalisar tarayya tsare shi ko ƙoƙarin cin zarafinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ƙarar, ya zargi majalisar tarayyar da gayyatarsa don bincike kan wani faifan murya da aka ce an nada a WhatsApp da ba a tabbatar da sahihancinsa ba.

Bobrisky ya ce majalisar ta kasa tantance gaskiyar sautin muryar duk da ƙalubalantar shi ta hannun lauyoyinsa, inda ya jawo masa damuwa.

Ya bayyana cewa binciken ya take haƙƙinsa, ya jefa shi cikin tsangwama, kuma ya fallasa shi ga barazana daga wasu da bai sani ba.

Dan daudu na neman diyyar N1.2bn

Dan daudun ya nemi kotun da ta tilasta a biya shi diyyar Naira biliyan 1.2, inda ya ke neman Naira miliyan 200 daga EFCC da Naira biliyan 1 daga majalisar tarayyar.

Kara karanta wannan

APC ta tura ƴan daba sun hargitsa zaben gwamnan jihar Ondo? Jam'iyya ta magantu

A cikin ƙarar, Bobrisky ya zargi hukumomin tsaro da tauye haƙƙin ɗan adam, yana mai kira ga duniya ta sa ido kan wannan dambarwar da ke faruwa.

Ya kuma caccaki ministan harkokin cikin gida kan ba da umarnin kama shi a kan iyakar Seme, wanda ya ce hakan ya janyo masa matsananciyar rashin lafiya.

Bobrisky ya tsere daga Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa shahararren dan daudu mai suna Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky ya samu damar ficewa daga tarayyar Najeriya.

An ce Idris Okuneye ya samu nasarar ficewa daga Najeriya ne bayan ya yi yunkurin fita daga kasar har sau biyu ba tare da samun nasara ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.