'Ba Su da Kaciya': Malamin Musulunci Ya Fadi Yadda Lakurawa Suka Yaudari Al'umma

'Ba Su da Kaciya': Malamin Musulunci Ya Fadi Yadda Lakurawa Suka Yaudari Al'umma

  • Wani malamin Musulunci a Sokoto, Sheikh Abdulbasit Silame ya fadi yadda Lakurawa suka yaudare su a jihar
  • Sheikh Silame ya ce tun farkon zuwan Lakurawa sun tabbatar musu cewa za su kawo karshen ta'addanci da ake yi a yankunansu
  • Sai dai daga bisani al'umma sun fahimci yaudara ce inda suma suka fara kai hare-hare kan al'umma da dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Babban malamin Musulunci a jihar Sokoto ya yi magana kan ayyukan yan kungiyar Lakurawa.

Sheikh Abdulbasit Silame ya bayyana yadda yan Lakurawa suka yaudari yan jihar da cewa za su taimaka musu.

Malamin Musulunci ya fadi yadda tsarin Lakurawa yake
Sheikh Abdulbasit Silame ya yi magana kan ta'addancin Lakurawa a Sokoto. Hoto: @Ahmedaliyuskt.
Asali: Twitter

Malamin Musulunci ya koka kan ayyukan Lakurawa

Malamin ya bayyana haka ne a ranar Juma'a 14 ga watan Nuwambar 2024, kamar yadda Tribune ta tabbatar a rahotonta.

Kara karanta wannan

'Ta burge ni': Abin da Sheikh Kabiru Gombe ya ce a liyafar auren yar Kwankwaso

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Silame ya ce Lakurawa sun yaudari mutane cewa za su kawo karshen ta'addancin da ake yi a yankin.

Ya tabbatar da cewa yan kungiyar sun shigo Najeriya ne ta bakin iyakar jihohin Sokoto da Kebbi.

"Sun zo ne tun farko cikin fara'a da mutane inda suka yi alkawarin za su ceto al'umma daga halin da suke ciki."
"Bayan wasu shekaru ne muka fahimci cewa sun yaudara mu ne kawai kuma babu maganar cetonmu sun zo domin mamaye yankunanmu."
"Ina tsammanin suna da wani nufi kan Hausa/Fulani saboda ba Fulani ba ne yan Nijar ne da Mali da Burkina Faso."

- Sheikh Abdulbasit Silame

'Ba su da kaciya a wandonsu' - Sheikh Silame

Shehin malamin daga bisani ya ce mafi yawan yan Lakurawa dogaye ne kuma sirara da suke yawo babu kaciya.

Ya tabbatar da cewa sun fahimci haka ne a gawar daya daga cikinsu wanda ke nuna ba su mu'amala da mata.

Kara karanta wannan

'Mun yi kokarinmu': Malamin Musulunci kan ragargazar Bello Turji da sojoji ke yi

Yadda Lakurawa ke sauya limamai a Sokoto

A baya, kun ji cewa wasu mazauna yankunan da Lakurawa suke sun yi magana kan ayyukan yan kungiyar a jihar Sokoto.

Al'umma sun tabbatar da cewa Lakurawa sun addabi wasu kananan hukumomi 5 a Sokoto inda suke sauya limamai idan ba su gamsar da su ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.