‘Yan Sanda Sun Ki Karbar Cin Hancin Naira Miliyan 174 daga Hannun ‘Dan Damfara

‘Yan Sanda Sun Ki Karbar Cin Hancin Naira Miliyan 174 daga Hannun ‘Dan Damfara

  • Ana zargin Patrick Akpoguma ya samu kudin da yake kashewa ne ta hanyar damfarar mutane a yanar gizo
  • Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bayyana cewa wanda ake zargi ya nemi ya ba jami’anta cin hanci da rashawa
  • Duk da kaurin $100, 000, ‘yan sanda sun ki karbar rashawar, sun dage sai sun gurfanar da shi a gaban kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Lagos - Jami’an ‘yan sandan Najeriya na reshen jihar Legas sun yi ikirarin sun yi watsi da tayin cin hanci daga wajen ‘dan damfara.

Dakarun ‘yan sandan sun ce wani da ake zargi da laifin damfara ta yanar gizo, Patrick Akpoguma, ya nemi ya ba su rashawar N174m.

'Yan sanda
Mai damfara ya shiga hannun ‘yan sanda Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Damfarar Patrick Akpoguma a yanar gizo

Jaridar The Nation ta ce Patrick Akpoguma ya yi suna wajen yaudarar mutane da sunan soyayya da satar kudi da tsafi ta yanar gizo.

Kara karanta wannan

'Ta burge ni': Abin da Sheikh Kabiru Gombe ya ce a liyafar auren yar Kwankwaso

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake magana a gaban ‘yan jarida a hedikwatar ‘yan sanda da ke Legas, Akpoguma ya amsa laifuffukan da ake zarginsa da aikatawa.

Ana zargin matashin ya nemi ya biya fam $100,000 domin hukuma ta wanke shi daga laifi.

A yanzu da Dalar Amurka ta tashi a sakamakon tsarin canjin kudi da bankin CBN ya kawo, fam $100,000 ta haura Naira miliyan 174.

'Yan sanda sun yi watsi da cin hanci

Duk da nauyin kudin da ya yi niyyar biya, jami’an tsaron sun ki karbar cin hancin su na masu tabbatar da jajircewarsu wajen zuwa kotu.

Babban jami’in ‘yan sanda, AIG Adegoke Fayoade ya ce an soma bincike tun ranar 7 ga watan Nuwamba da aka kawo karar matashin.

‘Yan sanda sun samu korafi ne daga wajen mazauna unguwar Lekki inda shi yake zaune, wannan bayani ya fito a jaridar nan ta Sun.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda aka cafke malamin asibiti da ke yiwa ‘yan bindiga magani a Katsina

Ana tuhumar Akpoguma da bude shafukan bogi a dandalin sada zumunta har ya kashe fam $11,200 saboda ya rika damfarar mutane.

An ce daga yaudarar jama’a da ya yi da sunan harkar Crypto ya saye kadarori a Legas da Edo da kuma mota kirrar GLE da ta kai N100m.

'Yan sanda sun cafke 'yan fashi a Kano

Labari ya gabata cewa jami'an 'yan sanda sun kama yan fashi da makami a Kano kuma an shirya gurfanar da su a gaban kuliya.

Ana zargin matasan da fashi a wasu yankunan jihar. ASP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce Haka zalika suna tare iyakokin wasu jihohi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng