Abin Kunya: An Fatattaki Dan Takarar Shugaban Kasa daga Gidan Haya a Bidiyo
- Duniya ta yiwa tsohon dan takarar shugaban kasa a APC daurin goro inda ya gaza biyan kudin haya da ake binsa tsawon shekaru
- An gano wasu jami'an kotu da yan sanda suna fatattakar Tunde Omosebi daga gidan haya a yankin Highbrow da ke birnin Abuja
- Mamallakin gidan da ya bukaci sakaya sunansa ya ce Omosebi ya shafe fiye da shekaru bai biya ko sisi ba da ake binsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - An fatattaki tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC a gidan haya da ke Abuja.
An kori Tunde Omosebi ne daga gidan da yake bayan shafe shekaru ba tare da ya biya basukan da ake binsa ba.
An kori dan takarar APC a gidan haya a Abuja
Wannan na kunshe ne a cikin wani faifan bidiyo da @MrLeasu ya wallafa a shafin X yayin da ake korar Omosebi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon, an gano wasu jami'an kotu da yan sanda suna korar dan takarar APC, Omosebi daga gidan da ke yankin Highbrow a Abuja.
Lamarin ya faru ne a ranar 15 ga watan Nuwambar 2024 inda mai gidan da ya boye sunansa ya ce kudin hayan ya dade da karewa.
Ya ce duk da kokarin da ya yi wurin tabbatar da Omosebi ya biya kudin hayar amma ya ki kuma ya ki ya bar gidan.
Har ila yau, mai gidan hayan ya ce ya gaji da hakuri na tsawon shekaru huɗu ba tare da kudi ba inda ya ce Omosebi kuma ya ki barin gidan.
Bidiyon yadda aka kori dan APC a gidan haya
Abba Kabir ya taimaki iyalan Ado Bayero
Kun ji cewa Gwamnatin jihar Kano ta kai dauki ga diyar marigayi Sarki Ado Bayero saboda bayyana fargabar za a kore ta da mahaifiyarta daga gidan haya da ta yi.
Gimbiya Zainab Ado Bayero ta nemi taimakon yayanta, Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero da na Sarki na 16, Muhammadu Sanusi II su gaza kar a kore su.
Amma a sakon da Darakta Kanar kan yada labaran gwamnatin Kano, Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce gwamna ya shiga lamarin.
Asali: Legit.ng