Dakarun Sojojin Sama Sun Samu Gagarumar Nasara kan 'Yan Bindiga

Dakarun Sojojin Sama Sun Samu Gagarumar Nasara kan 'Yan Bindiga

  • Dakarun sojojin saman Najeriya na rundunar Operation Fansan Yamma sun yi ruwan wuta kan maɓoyar ƴan bindiga a jihar Kaduna
  • Jami'an tsaron sun kai hare-hare a mafakar ƴan bindiga da ke tsaunin Dunya da dajin Batauna a ƙaramar hukumar Giwa ta jihar
  • Kakakin rundunar sojojin saman Najeriya ya bayyana cewa hare-haren sun yi sanadiyyar hallaka ƴan bindiga masu yawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Dakarun sojin sama na rundunar Operation Fansan Yamma sun ragargaji ƴan bindiga a jihar Kaduna.

Dakarun sojojin saman sun tarwatsa wata babbar maɓoyar ƴan bindiga da ke tsaunin Dunya da dajin Batauna a ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Sojoji sun ragargaji 'yan bindiga a Kaduna
Sojojin sama sun lalata maboyar 'yan bindiga a Kaduna Hoto: Sodiq Adelakun
Asali: Getty Images

Daraktan hulɗa da jama’a da yaɗa labarai na rundunar sojojin saman Najeriya, Air Commodore Olusola Akinboyewa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Abuja, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi ta'addanci, sun hallaka tsohon kansila har lahira

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojoji suka fatattaki ƴan bindiga

Akinboyewa ya ce, an kai harin ne a ranar 12 ga watan Nuwamba domin ci gaba da aikin kai hare-hare ta sama a yankin Arewa maso Yamma da aka yi wa laƙabi da “Operation Farautar Mujiya”.

A cewarsa, yankunan da aka kai hare-haren sun daɗe suna zama mafaka ga ƙungiyoyin ƴan bindiga saboda bishiyoyi da duwatsun da ke wuraren.

Akinboyewa ya ce maƙasudin kai hare-haren ta sama shi ne domin wargaza ƴan bindigan ta yadda ba za su iya taɓuka komai ba.

Ya ce harin na sama ya yi sanadiyyar kashe mayaƙa da dama tare da lalata tarin makamai da kayayyakin da ke da matuƙar muhimmanci ga ayyukan ƴan bindigan.

"Tun bayan da aka fara wannan aikin, majiyoyi masu sahihanci daga al'ummomin yankin sun tabbatar da cewa ƴan bindigan sun ci gaba da tserewa daga maɓoyarsu."

- Air Commodore Olusola Akinboyewa

Kara karanta wannan

An rasa rayuka bayan 'yan bindiga sun farmaki sojoji a wani shingen bincike

Ƴan bindiga sun farmaki sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa bindiga sun kai farmaki a sansanin sojoji da safiyar ranar Laraba, 13 ga watan Nuwamban 2024 inda suka hallaka jami'an tsaro mutum biyu a jihar Abia.

Ƴan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Ekenobizi a yankin Umuopara wanda ke kan iyaka da jihohin Imo da Abia.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng