Zaben Ondo 2024: Mataimakin Dan Takarar PDP Ya Hango Gagarumar Matsala

Zaben Ondo 2024: Mataimakin Dan Takarar PDP Ya Hango Gagarumar Matsala

  • Ɗan takarar mataimakin gwamna na jam'iyyar PDP a zaɓenn Ondo ya nuna damuwa kan ɓullar ƴan daba
  • Mista Festus Akingabaso ya zargi APC da ɗauko ƴan daba waɗanda suka mamaye wasu ƙauyuka ƙaramar hukumar Idanre ta jihar
  • Ya buƙaci jami'an tsaro da su shawo kan matsalar tare da tabbatar da cewa an gudanar da zaɓen cikin lumana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Mataimakin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Ondo, Mista Festus Akingbaso, ya nuna damuwa kan zaɓen gwamnan jihar.

Mista Festus Akingbaso ya nuna damuwa ne game da ƙwararar ƴan daba a ƙaramar hukumar Idanre a yayin zaɓen gwamnan da ake gudanarwa a jihar.

Mataimakin dan takarar PDP ya koka kan zaben Ondo
Mataimakin dan takarar PDP ya yi zargin an kawo 'yan daba Hoto: Festus Akingbaso
Asali: Facebook

Akingbaso wanda ɗan majalisar wakilai ne ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan kaɗa ƙuri’arsa a rumfar zabe mai lamba 005, a Oke Imikan, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi ta'addanci, sun hallaka tsohon kansila har lahira

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me mataikin ɗan takarar PDP ya ce kan zaɓen?

Ɗan majalisar ya bayyana jin daɗinsa kan yadda masu kaɗa ƙuri’a suka fito da kuma yadda aka samar da tsaro a rumfar zaɓensa.

Ya bayyana fargabarsa kan rahotannin cewa ƴan daba na kawo cikas a harkokin zaɓe a yankin.

Ya yi zargin cewa ƴan daban waɗanda aka shigo da su cikin dare a Idanre, na yi wa jam'iyyar APC mai mulki a jihar aiki ne.

"Bayanan da suka zo min sun nuna cewa ƴan daban da ake zargin APC ce ta kawo su sun mamaye ƙauyuka da dama."
"Rahotanni sun ce an mamaye ƙauyuka irin su Ofosun da Omifunfun. A Igbepo, wasu da ake zargin ƴan daba ne suna nan sun yi gungu."

- Festus Akingbaso.

Ɗan takarar mataimakin gwamnan na jam’iyyar PDP ya yi kira ga jami’an tsaro da su shawo kan lamarin tare da tabbatar da gudanar da zaɓen cikin lumana a yankunan da lamarin ya shafa.

Kara karanta wannan

Ondo 2024: Hukumar zaɓe INEC ta canza ɗan takarar gwamna ana gobe zaɓe

Gwamna ya kaɗa ƙuri'arsa a zaɓen Ondo

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Ondo Lucky Aiyedatiwa na jam'iyyar APC ya kaɗa kuri'arsa a zaben gwamnan da ke gudana a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba a jihar Ondo.

Gwamnan wanda ke takara a inuwar jam'iyyar APC ya jefa ƙuri'arsa a rumfar zaɓe mai lamba 5 da ke gunduma ta 5, Obenla a karamar hukumar Ilaje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng