‘Ta Burge Ni’: Abin da Sheikh Kabiru Gombe Ya Ce a Liyafar Auren Yar Kwankwaso

‘Ta Burge Ni’: Abin da Sheikh Kabiru Gombe Ya Ce a Liyafar Auren Yar Kwankwaso

  • A yau Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024 za a daura auren yar Sanata Rabiu Kwankwaso da dan Alhaji Dahiru Mangal
  • An gudanar da liyafar bikin a jiya Juma'a 15 ga watan Nuwambar 2024 wanda ya samu halartar Sheikh Kabiru Gombe
  • Hakan ya jawo ce-ce-ku-ce daga wasu yan Najeriya da suke ganin bai dace malamai su halarci wurin da ke da maza da mata ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Yan Najeriya da dama sun yi ta korafi da Sheikh Kabiru Gombe ya halarci liyafar auren yar Sanata Rabiu Kwanwkaso.

Mutane sun yi ta korafi kan yadda malaman Musulunci za su halarci bikin da aka cakuda maza da mata.

Bidiyon Sheikh Kabiru Gombe ya jawo magana a liyafar auren yar Kwankwaso
Sheikh Kabiru Gombe ya yaba da shigar da yar Rabiu Kwankwaso ta yi. Hoto: Karatuttukan Malaman Sunnah.
Asali: Facebook

Sheikh Kabiru Gombe ya yaba yar Kwankwaso

Shafin karatuttukan malaman sunnah ya wallafa bidiyo inda Sheih Kabiru ke magana game shigar amaryar.

Kara karanta wannan

'Mun yi kokarinmu': Malamin Musulunci kan ragargazar Bello Turji da sojoji ke yi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin faifan bidiyon, Sheikh Gombe ya ce shigan amaryar mai suna Dr. Aisha Rabiu Kwankwaso ya yi matukar burge shi.

Shehin Malamin ya bukaci a yi koyi da irin shigarta duba da yadda ta rufe jikinta tun daga sama har kasa.

Sheikh Kabiru ya fadi hazakar ango Fahad

"Wani abu ya ba ni sha'awa a wannan taro kwarai da gaske lokacin da ango da amarya suka shigo wurin taro, na ga amarya ta rufe jikinta daga sama har kasa."
"Ina ma ace amare a bukukuwansu za su yi koyi da Aisha a gansu sun shiga cikin sutura irin wacce da dace."
"Ango Fahad, yana cikin dalibanmu, dalibi ne mai kokari ya yi karatun boko mai zurfi, ya yi karatun addinin Musulunci, in Allah ya yarda, Aisha kin samu abokin zama da za ku taru ku gina zuri'a"

- Sheikh Kabiru Gombe

Sheih Kabiru Gombe ya magantu kan zanga-zanga

Kara karanta wannan

Zuwa bikin 'liyafa' da malamai suka yi na auren yar Kwankwaso ya tayar da kura

A baya, kun ji cewa Sakataren ƙungiyar Izala, Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe ya yi magana kan zanga-zangar da matasa ke shiryawa.

Shehin Malamin ya yi kira ga matasa su rungumi zaman lafiya kana su guji duk wani abu da zai iya haifar da tashin hankali.

Sheikh Kabiru ya bayyana cewa manyan addinai Musulunci da Kiristanci sun koyar da bin hanyar lalama wajen warware kowace irin matsala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.