Zuwa Bikin ‘Liyafa’ da Malamai Suka Yi na Auren Yar Kwankwaso Ya Tayar da Kura

Zuwa Bikin ‘Liyafa’ da Malamai Suka Yi na Auren Yar Kwankwaso Ya Tayar da Kura

  • Yan Najeriya da dama sun yi martani da aka gano wasu malaman Musulunci a wurin bikin 'dinner' na auren yar Rabiu Kwankwaso
  • Hakan ya tayar da kura inda wasu ke ganin bai kamata malamai da suke kushe lamarin ba kuma za a gansu a wurin
  • Wannan na zuwa ne bayan shirin daura auren yar Kwankwaso da kuma dan attajiri, Alhaji Dahiru Mangal a yau Asabar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - A yau Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024, Sanata Rabiu Kwankwaso zai aurar da yarsa, Dr. Aisha Rabiu Musa.

Dr. Aisha Musa za ta auri angonta wanda 'da ne ga fitaccen attajiri, Alhaji Dahiru Mangal wanda ake kira Fahad Dahiru Mangal.

An soki malaman da suka halarci bikin 'dinner' a auren yar Kwankwaso
Yan Najeriya da dama sun caccaki malaman da suka je bikin 'dinner' a auren yar Rabiu Kwankwaso. Hoto: Karatuttukan Malaman Sunnah.
Asali: Facebook

Sheikh Kabiru Gombe ya fadakar da mutane

Karatuttukan Malaman Sunnah ta wallafa bidiyon Sheikh Kabiru Gombe da Ahmad Sulaiman suna fadakarwa yayin bikin 'liyafa' a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

'Mun yi kokarinmu': Malamin Musulunci kan ragargazar Bello Turji da sojoji ke yi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai yan Najeriya da dama sun yi Allah wadai da halartar 'liyafa' da malaman suka yi duba da yadda aka cakuda maza da mata.

Wasu sun fara kokwanto kan yadda malaman za su fadakar da mabiyansu kan haramci ko halaccin zuwa liyafar.

Martanin wasu kan halartar malaman bikin 'dinner'

Abubakar Musa:

"Allah ya jikan Malam Idris ba dan ya mutu ba, domin girman Allah ta yaya mutum zai ki Malam Idris idan dai ba son zuciya ba?"

Abubakar Sadeeq:

"Tabdi jam malamai da zuwa wurin 'dinner' ta ya za ku yiwa dalibai wa'azi su ji ku?"

Mikail Shuwa:

"Allah ya karawa Malam Idris lafiya da nisan kwana, ikon Allah malaman sunna a wajen 'dinner' da aka hada maza da mata."

Shuaibu brahim:

"Daman malamai suna zuwa wajen 'dinner' da aka hada maza da mata?"

Abakar Sadeeq Godowoli:

"Ni wallahi ma na ji kunya."

Mohammed Nasir Ali:

"Mallam lallai an tafka kuskure a nan gaskiya, taron maza da mata a hade bai kamata kuna wajen ba, Allah ya ba su zaman lafiya."

Kara karanta wannan

Chiroman Kano: Sanusi II ya fadi dalilin zaben dansa da ya nada saurata mai daraja

Wannan ya biyo bayan yaba shigar Amarya da Sheikh Kabiru Gombe ya yi da cewa ta burge shi matuka inda ya bukaci a rika koyi da irinsu.

Manyan baki sun hallara domin auren yar Kwankwaso

Kun ji cewa manyan baki sun fara isa Kano domin shaida auren yar Sanata Rabi'u Kwankwaso da za a daura a gobe Asabar, 16 ga watan Nuwamba.

Tsofaffin gwamnoni daga jihohi daban daban sun isa Kano yayin da jagoran NNPP ya karɓe su a gidansa bayan kammala sallar Juma'a.

Za a daura auren Dr Aisha Rabi'u Musa Kwankwaso ne da Fahad Dahiru Mangal a fadar mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.