Tsohon Shugaban DSS Ya Yi Magana kan Ƴan Ta'addan Lakurawa, Ya Faɗi Wanda Ya Gayyato Su
- Tsohon shugaban hukumar DSS, Mike Ejiofor ya ce ƙungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta Lakurawa ba sabuwa ba ce a Najeriya
- Ejiofor ya bayyana cewa wani basarake a jihar Sakkwato ne ya gayyato su da kyakkyawar niyya domin su taimaka ba tare da sanin manufarsu ba
- Ya bayyana cewa ƴan kungiyar ta'addancin Lakurawa ba ƴan Najeriya ba ne, sun fito daga jamhuriyar Nijar da Mali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Tsohon daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), Mike Ejiofor, ya ce kungiyar ‘yan tada kayar baya Lakurawa da ke kai hare-hare a Arewa ba sabuwa ba ce.
Ejiofor ya bayyana cewa ƙungiyar Lakurawa, mai tsattsauran ra'ayin addini ta jima tana ayyukanta a shiryyar Arewa maso Yamma.
Tsohon daraktan ya faɗi haka ne da yake jawabi a cikin shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels ranar Jumu'a, 15 ga watan Nuwamba, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
DHQ ta tababatar da ɓullar ƴan Lakurawa
A makon da ya gabata ne hedkwatar tsaro ta sanar da bullar Lakurawa a matsayin wata sabuwar kungiyar ta’addanci a jihohin Sakkwato da Kebbi.
Daraktan yada labarai na DHQ, Manjo Janar Edward Buba, ya ce kungiyar ta'addancin na kara ta'azzara rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma.
Buba ya ƙara da cewa a halin yanzu dakarun sojoji sun tarfa ƴan Lakurawa da nufin kawo ƙarshensu gaba ɗaya.
Tsohon shugaban DSS ya magantu kan Lakurawa
Da yake tsokaci kan lamarin, tsohon daraktan DSS, Nike Ejiofor ya ce ƴan ƙungiyar Lakurawa ba ƴan Najeriya ba ne, sun fito ne daga ƙasashen Mali da Nijar.
“Na yi mamaki da na ji cewa Lakurawa wata sabuwar kungiyar ta’addanci ce, a zahirin gaskiya ba sabuwa ba ce.
"Tsohon shugaban mulkin soji a Jamhuriyar Nijar, Ibrahim Baré Maïnassara ne ya kirkiro kungiyar a matsayin ƴan sa'kai, suna taimaka masa a lokacin.
"Bayan ya mutu gwamnatin Jamguriyar Nijar ta yi watsi da su, daga nan kuma suka tarwatse. Wani hakimi a Sokoto ya gayyace su don taimaka musu da kyakkyawar niyya, ba tare da sanin suna da wata manufa ba.”
- Mike Ejiofor.
Lakurawa ta karɓe matsayin sarakuna
A wani rahoton, an ji cewa yan ta'addan kungiyar Lakurawa sun karɓe ayyukan sarakunan gargajiya a kauyukan Kebbi da ke Arewa maso Yamma.
Bulama Bukarti ya ce a yanzun duk tafiyar kilomita biyar a kowace ƙaramar hukuma a jihar Kebbi sai ka haɗu da Lakurawa.
Asali: Legit.ng