Chiroman Kano: Sanusi II Ya Fadi Dalilin Zaben Dansa da Ya Nada Saurata Mai Daraja
- Sarkin Kano, Mai Martaba Muhammadu Sanusi II ya fadi musabbabin zaben dansa a matsayin Chiroman Kano
- Sanusi II ya ce ya yaba da halayen dan nasa, DSP Aminu Lamido Sanusi da kuma irin taimakon al'umma da yake yi
- Wannan na zuwa ne bayan nadinsa Chiroman Kano a yau Juma'a 15 ga watan Nuwambar 2024 a fadar Mai Martaba Sanusi II
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Dandazon al'umma sun cika fadar Sarki Muhammadu Sanusi II domin halartar bikin nadin sarauta.
A yau Juma'a 15 ga watan Nuwambar 2024 aka yi bikin nadin DSP Aminu Lamido Sanusi a matsayin Chiroman Kano.
Muhammadu Sanusi II ya nada dansa Chiroman Kano
Leadership ta ce sarautar Chiroma tana da matukar tasiri da muhimmanci da ke kula da wasu masarautu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin bikin, Sarki Muhammadu Sanusi II ya fadi dalilin nadin Aminu sarautar Chiroman Kano.
Basaraken ya an nada shi ne duba da yadda yake biyayya ga masarautar da taimakon al'umma da kuma gudunmawa ga mutane.
"Na zabi in karrama shi da wannan sarauta saboda halayensa da kuma taimakon al'umma da yake yi."
"Ka gaji sarautar Chiroman Kano daga kakanka, kuma kai ne na 17, na bukace ka da ka kasance mai bin hanya ingantacciya."
- Muhammadu Sanusi II
Bikin nadin sarautar ya samu halartar manyan mutane cikin har da Gwamna Abba Kabir na jihar Kano.
Sannan mataimakin gwamna, Abdulsalam Gwarzo shi ma ya halarci taron da manyan malamai da sarakunan gargajiya da manyan yan kasuwa.
Hotunan nadin sarautar Chiroman Kano a yau
Masarautar Kano ta wallafa yadda bikin ya wakana cikin hotuna a shafinta na X a yau Juma'a 15 ga watan Nuwambar 2024.
Sanusi II ya shawarci alkalai a Najeriya
Kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi magana kan halayen wasu daga cikin alkalai da ke hukuncin zalunci.
Sarki Sanusi II ya shawarci alkalan da su tabbatar da yin adalci a dukan hukunce-hukunce da za su yi ba tare da wariya ba.
Basaraken ya tuna musu ranar gobe inda ya ce idan ba su yi adalci a duniya ba wa zai tsaya musu a wancan rana.
Asali: Legit.ng