Babban Alƙalin Jihar Yobe Zai Dawo da Albashin Shekaru 12, An Dakatar Wasu 2
- Hukumar shari'a ta kasa ta dakatar da wasu alkalan manyan kotunan jihohin Anambra da kuma Rivers a Najeriya
- Hukumar ta kuma tura sunayen alkalan manyan kotunan Yobe da Imo domin yi musu ritayar dole tare da dawo da albashinsu
- Wannan na zuwa ne bayan zargin manyan alkalan kotun jihohin Imo da Yobe da ba da bayanan karya game da shekarunsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Hukumar shari'a ta kasa (NJC) ta bukaci yin ritayar dole ga alkalan manyan kotunan jihohi.
Hukumar ta tura sunayen alkalan manyan kotun jihohin Imo da Yobe kan zargin ba da bayanan karya kan shekarunsu.
Ana zargin alkalai da zamba a shekarunsu
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Kemi Babalola-Ogedengbe ya fitar, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alkalan kotun da abin ya shafa su ne Mai Shari'a, Chukwuemeka Chikeka daga babbar kotun Imo da kuma Kadi Babagana Mahdi a jihar Yobe.
An samu Mahdi da ba da shekarun karya da kuma ranar haihuwa mabanbanta da suka ci karo da juna wanda ya saɓa ka'ida.
Daga bisani, za a tura bukatar ritayar dole ga Mahdi tare da dawo da albashin shekaru 12 da alawus, Punch ta ruwaito.
An dakatar da manyan alkalan kotu 2
Hukumar NJC ta kuma dakatar da babban alƙalin kotun jihar Rivers, G. C. Aguma daga aiki.
Hukuncin ya ce alkalin zai shafe akalla shekara daya ba tare da samun albashi ba inda aka kakaba masa shekaru biyu da za a rika sanya masa ido.
Har ila yau, an dakatar da A. O. Nwabunike daga alkalanci a jihar Anambra daga gudanar da lamuran shari'a.
Babban alƙali ya kubuta daga yan ta'adda
Kun ji cewa mai shari'a Haruna Mshelia wanda ake tunanin ƴan ta'addan Boko Haram ne suka sace shi, ya shaƙi iskar ƴanci.
Alƙalin babbar kotun jihar Borno ya kuɓuta ne a ranar Asabar, 7 ga watan Satumbar 2024 bayan ya kwashe watanni biyu a tsare a hannun miyagun.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng