Lagbaja: A Karshe, An Birne Gawar Marigayi Tsohon Hafsan Sojoji a Abuja

Lagbaja: A Karshe, An Birne Gawar Marigayi Tsohon Hafsan Sojoji a Abuja

  • A karshe, an birne gawar marigayi shugaban rundunar sojojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja a makabartar kasa da ke Abuja
  • Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu Tinubu, da mataimakinsa, Kashim Shettima na cikin manyan ƙasa da suka halarci jana'iza
  • A wurin taron wanda ya shafe sama da sa'o'i biyu, Tinubu ya karrama Lagbaja da lambar yabo ta ƙasa CFR kwanaki bayan ya bar duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Rahotanni sun yi nuni da cewa an kammala jana'izar marigayi shugaban rundunar sojojin ƙasa ta Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.

A yau Juma'a, 15 ga watan Nuwamba, 2024 aka birne tsohon COAS a gaban manyan ƙasar nan a babbar maƙabarta ta kasa da ke Abuja.

An birne Lagbaja a Abuja.
An kammala jana'izar marigayi shugaban sojojin ƙasa, Taoreed Lagbaja Hoto: @HQNigeriaArmy
Asali: UGC

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, hakan ne ya kawo ƙarshen bukukuwan jana'izar da aka shafe kwanaki biyu ana yi.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban DSS ya y magana kan ƴan ta'addan Lakurawa, ya faɗi wanda ya gayyato su

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An birne gawar marigayi Taoreed Lagbaja

An ruwaito cewa an birne gawarsa a cikin ƙasa da misalin karfe 4:41 na yammacin yau Jumu'a a wurin taron jana'iza da ya shafe sama da sa'o'i biyu.

Akwatin gawar Lagbaja, wanda aka lullube da tutar Najeriya mai launin kore da fari, ya isa makabartar da misalin karfe 3:00 na yamma a cikin wata farar motar jana'iza.

A wurin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da karrama marigayin da lambar yabon CFR ta ƙasa domin yabawa hidimar da ya yi wa ƙasa.

Lagbaja: Manyan shugabanni sun halarci wurin

Baya ga Shugaba Tinubu, an ga manyan kusoshin gwamnati da jami'an sojoji a wurin jana'izar Lagbaja.

Daga cikin waɗanda suka halarci wurin har da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da ministan tsaro, Muhammad Abubakar Badaru.

An ga babban hafsan hafsoshin tsaron kasar nan, CDS Christopher Musa, muƙaddashin hafsan sojojin kasa, Olufemi Oluyede, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

Lagbaja: Shugaba Tinubu ya karrama marigayi hafsan sojojin ƙasa a wurin jana'iza

Pantami ya yi alhinin mutuwar Lagbaja

A wani rahoton, kun ji cewa Farfesa Isa Ibrahim Pantami ya yi alhinin rashin da aka yi na babban hafsan sojojin ƙasa (COAS), Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.

Tsohon ministan na sadarwa ya bayyana marigayin a matsayin wanda ya ba da gudunmawa wajen wanzar da zaman lafiya a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel