Lagbaja: Shugaba Tinubu Ya Karrama Marigayi Hafsan Sojojin Ƙasa a Wurin Jana'iza
- Bola Ahmed Tinubu ya karrama marigayi shugaban rundunar sojojin ƙasa, Taoreed Lagbaja da lambar yabo ta kasa CFR
- Shugaban ƙasar ya ce Lagbaja na ɗaya daga cikin mutanen da yake alfahari .da naɗinsu bayan hawansa kan madafun iko
- Manyan kusoshin gwamnatin tarayya da jami'an sojoji sun halarci jana'izar COAS a babbar maƙabartar ƙasa da ke Abuja ranar Juma'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Ahmed Tinubu ya halarci jana'izar marigayi hafsan rundunar sojojin ƙasa ta Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.
Shugaba Tinubu ya karrama marigayi shugaban sojojin da lambar yabon CFR ta ƙasa a wurin jana'izarsa yau Juma'a, 15 ga watan Nuwamba, 2023.
Shugaba Tinubu ya karrama Lagbaja
Channels tv ta tattaro cewa Tinubu ya sanar da hakan ne a wurin bikin jana'izar. marigayi COAS a makabartar kasa da ke Mogadishu, Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ƙasar ya yaba da kyawawan halayen marigayi gwarzon sojan, inda aka ji yana faɗin irin gudummuwar da ya bayar a harkokin tsaron Najeriya.
A cewar Bola Tinubu, nadin Marigayi Lagbaja a matsayin COAS na daya daga cikin mafi kyawun naɗe-naɗen da ya yi kawo yanzu.
Mutuwar hafsun sojojin ƙasa
A makon da ya gabata, Shugaba Tinubu ya sanar da rasuwar Lagbaja, inda ya ce marigayi COAS ya rasu ne a Legas bayan ya yi fama da rashin lafiya.
An haife shi a ranar 28 ga Fabrairu, 1968, Lagbaja ya rike mukamin babban hafsan soji na tsawon shekara daya da wata hudu daga lokacin da Tinubu ya naɗa shi a Yuni, 2023.
Lagbaja: Manyan kusoshi sun halarci jana'iza
Jana'izar marigayin tsohon shugaban sojojin ta samu halartar mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.
Kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ministan tsaro, gwamnoni da manyan jami'an soji sun halarci bikin birne Lagbaja yau Juma'a a Abuja, in ji Daily Trust.
Tinubu ya fara shirin naɗa sabon COAS
A wani labarin, kun ji cewa bayan rasuwar babban hafsan sojojin kasar nan, Laftanar Janar .Taoreed Lagbaja, ana jiran a fadi wanda zai maye gurbinsa.
Ana sa ran za a bayyana Laftanar Janar Oluyede a matsayin sabon babban hafsan soji bayan jim kadan daga likkafarsa a rundunar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng