NBS: Farashin Abinci Ya Yi Tashin Gwauron Zabo, Ya Yi Tsalle da zuwa 33.8% a 2024
- Hukumar kididdiga ta kasa ta fitar da rahoton da ya bayyana samun hauhawar farashin kayan abinci a watan Oktoba
- Hauhawar farashin ya biyo bayan karuwar kudin wasu daga cikin kayan abinci kamar shinkafa da doya a kasuwanni
- An samu karin farashi da akalla 32.7% a cikin watan Satumba, kuma ya haura zuwa 33.88% a watan Oktoba, 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Hukumar kididdiga ta kasa ta bayyana cewa an samu hauhawar farashi a fadin kasar nan.
Hukumar ta kara da bayyana cewa an samu karin da akalla 32.7% a watan Satumba, kuma ya haura zuwa 33.88% a watan Oktoba, 2024.
Jaridar The Cable ta wallafa cewa an tabbatar da samun karuwar farashin bayan tattara alkaluma daga farashin abinci da sauran ayyuka a kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"An samu hauhawar farashi:" NBS
An samu hauhawar kayayyaki da na abinci a Najeriya, wanda ya haura da 1.8% a watan Oktoba idan aka kwatanta da watan da ya gabace shi.
Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta kara da cewa wannan na nufin an samu karuwar hauhawar farashi da 6.55% idan aka kwatanta da watan Oktoba, 2023.
NBS ya fadi dalilin hauhawar farashi
Hukumar NBS ta bayyana cewa tsadar farashin kayan abinci kamar doya da shinkafa sun jawo hauhawar farashi da 39.16% a watan Oktoba.
Sauran kayan da farashinsu ya daga sun hada da masara, burodi, man ja da man gyada, gwaza (makani) da dai sauransu.
Wannan ya haura yadda aka san hauhawar farashin kayan abinci da ya kai percent 33.77% a watan Satumba, 2024.
NBS: Farashin kayan abinci ya sauko
A baya kun ji cewa hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta bayyana cewa farashin kayan abinci ya sauko da 33.40% a watan Yuli idan aka kwatanta da watanni 19 da suka gabata.
Rahoton da hukumar NBS ta fitar ya gano cewa farashin kifi, dodon kodi, dabino, kankana, garri, littattafai, nama da dai sauran wasu kayayyakin abinci da na amfani ya sauka sosai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng