'Yadda Manufofin Tinubu Za Su Amfani Miliyoyin ƴan Najeriya,' Minista Ya Yi bayani
- Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris ya ce manufofin gwamnati za su inganta rayuwar miliyoyin jama'a
- Alhaji Mohammed Idris ya lissafa shirye-shiryen gwamnati na gina al'umma da suka hada da CCC, tallafin gine-gine da sauransu
- A wani taro a Abuja, gwamnatin tarayya ta bukaci masu tallace tallace da su kiyaye al'adun kasa da tallafawa masu kirkira
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa manufofin Shugaba Bola Tinubu za su samar da ingantacciyar rayuwa mai dorewa ga miliyoyin ‘yan Najeriya.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Alhaji Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a yayin taron tallace-tallace na kasa da aka gudanar a Abuja.
Minista ya magantu kan manufofin Tinubu
Idris wanda Lanre Issa-Onilu, darakta janar na NOA ya wakilta, ya bayyana mahimmancin tsaron yanar gizo ga masu talla da kirkira, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron mai taken "Tafiya da zamani: Fasaha, al'adu da sababbin hanyoyin kasuwanci," ya nuna muhimmancin daidaita tallace-tallace da sauye-sauyen al'adu da fasahohin Najeriya.
Ministan ya bayyana tsare-tsaren gwamnati, kamar shirin ba da lamuni, shirin CCC, da tallafin gine gine ne Renewed Hope a matsayin shirye-shiryen bunkasa jama'a.
Gwamnati ta nemi hadin kan masu talla
Alhaji Mohammed Idris ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta ba da fifiko ga ababen more rayuwa, da suka hada da tituna, layin dogo, da tashoshin jiragen ruwa.
Ya yi kira ga masu talla da su kiyaye manufofin gwamnati domin samun ci gaba a bangaren isar da saƙo, samun yardar abokan hulda da sauran tallafi daga gwamnati.
Ministan ya nuna tasirin hanyoyin sadarwa na zamani da suka ba masu tallace tallace damar isar da sako ga mutane cikin sauki, yayin da ya nuna damuwa kan yaduwar labaran karya.
Gwamnati ta gargadi masu tallace tallace
Ya gargadi masu talla da su ba da fifikon ga da'a da kuma amfani da fasahohin zamani wajen samun yardar abokan huldarsu da ma masu ruwa da tsaki a fannin.
Trust Radio ta rahoto ministan ya jaddada rawar da tallace-tallace ke takawa wajen magance matsalar bambancin al'adu ta hanyar isar da sakonnin da suka dace da zamantakewa.
A ƙarshe, ya bukaci masu tallace-tallace da su rika sanya al'adun Najeriya, tallafawa masu kirkira na gida, da kuma yada kyawawan labaran Najeriya ga duniya.
Tinubu ya fitar da sababbin tsare tsare
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta fitar da sanarwa kan wasu tsare tsare da ta kawo a kan tattalin arzikin Najeriya.
Hadimin shugaban kasa a kan tsare-tsaren haraji, Taiwo Oyedele ya bayyana cewa za a gabatar da kudirin sabon tsarin a gaban majalisa domin amincewa.
Asali: Legit.ng