'Yan Sandan Kano Sun Kama Yan Fashi da ke Tare Hanyoyi a Jihohin Arewa

'Yan Sandan Kano Sun Kama Yan Fashi da ke Tare Hanyoyi a Jihohin Arewa

  • Rundunar yan sandan jihar Kano ta kara karfafa matakai domin yakar yan fashi da makami da sauran miyagu
  • Kakakin yan sandan jihar Kano ya bayyana wata nasara da suka samu a kan wasu yan fashi da makami
  • DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce ana zargin miyagun da fashi da makami a jihohin Arewacin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta samu nasara kan wasu yan fashi da makami.

Bayanan yan sanda ya tabbatar da cewa ana zargin yan fashin da tare iyakokin jihohi domin sata wa al'umma.

Yan fashi
An kama gundun yan fashi. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Legit tattaro bayanai kan kama miyagun ne a cikin wani sako da kakakin yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Sojoji sun saki wuta ta sama da kasa kan Lakurawa, miyagu sun fara gudu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama yan fashi da makami a Kano

Rundunar yan sandan jihar Kano ta sanar da cafke wasu matasa hudu da ake zargin su da fashi da makami a jihohi.

Yan sanda sun bayyana cewa ana zargin matasan da tare hanyoyi a wasu yankunan Kano, Jigawa da Bauchi.

Haka zalika an kama gungun masu fashi da makamin dauke da makamai da suka hada da bindigogi.

"Su ne yan fashin da suke tare hanyar Wudil, Gezawa, Gabasawa da iyakokin Kano-Jigawa da Kano-Bauchi
Mun samu bindiga kirar AK-47 a wajensu da wasu bindigogi guda uku kirar gida."

- Abdullahi Haruna Kiyawa

Ana sa ran cewa rundunar yan sanda za ta gurfanar da su a gaban alkali domin yi musu hukunci da zarar an kammala bincike.

Yan Najeriya a kafar sada zumunta sun yabawa yan sandan jihar Kano bisa kokarin cafke miyagun da suka yi.

An kama yan fashi a jihar Edo

Kara karanta wannan

Lakurawa sun ji ruwan alburusai, sun fara guduwa daga Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sanda a jihar Edo ta tabbatar da kama wasu mutane hudu da ake zargi sun yi fashi da makami a gidan wani mutum.

Bayanan yan sanda sun tabbatar da cewa an yi fashi da makamin ne a Ibie ta Kudu a karamar hukumar Etsako ta Yamma a Edo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng