'An Gyara Layukan Wutar,' TCN Ya Fadi Halin da Lantarkin Arewa Take ciki Yanzu
- Kamfanin wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya dawo da wutar lantarki zuwa layin 330kV na Ugwuaji-Apir bayan gyare-gyare
- TCN ya bayyana cewa dawo da wuta a kan layin zai inganta samar da wutar lantarki a Arewa maso Gabas da Arewa ta Yamma
- Kamfanin ya tabbatar da cewa injiniyoyi sunyi aiki tukuru wajen gano matsalar da kuma warware ta cikin kankanin lokaci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kamfanin wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da dawo da wutar lantarki a layin wutar Ugwuaji-Apir mai ƙarfin 330kV.
A ranar 22 ga Oktoba, TCN ta bayar da rahoton rashin wuta a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, sakamakon matsala a layukan lantarki biyu.
TCN ya gayara wutar lantarkin Arewa
Bayan kwanaki biyu, ma’aikatan TCN sun gano matsalar da ta janyo ƙarancin wuta a layukan wutar guda biyu tare da fara aikin gyarawa, inji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar 30 ga Oktoba, TCN ta dawo da wuta ga jihohi bakwai na Arewa ta layin daya, wanda ya ba da damar samun wuta a wadannan jihohi.
A sanarwa ta baya-bayan nan, Ndidi Mbah, mai magana da yawun TCN, ta tabbatar da dawo da wuta ga layin biyu da a ranar Alhamis.
Arewa za ta samu karuwar wuta
Ndidi Mbah ta ce yanzu da wuta ta dawo kan layukan biyu, kamfanonin rarraba lantarki na Jos, Kaduna, Kano, da Yola za su samu karin wutar.
Ta kuma ce, “TCN ta kammala gyare-gyaren layin da aka lalata, wanda ya bai wa injiniyoyinmu damar dawo da wutar."
Yanzu haka, tashoshin lantarki na Apir da Jos sun fara karɓar karin lodin wuta, wanda zai samar da karuwar wuta ga yankunan da abin ya shafa.
TCN ya aika sako ga mutanen Arewa
Layukan wutar Ugwuaji-Apir ya daina aiki tun daga ranar 21 ga Oktoba, sakamakon lalacewar wayoyin wutar, kafin a gyara tare da mayar da wuta kan layin farko.
Yanzu da aka layi na biyu ya samu wuta, dukkanin layukan suna aiki, wanda zai inganta samar da wuta a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.
Ndidi Mbah ta gode wa jama’ar yankunan da abin ya shafa saboda hakurinsu a wannan mawuyacin yanayi na rashin wuta, tana mai jinjinawa juriyar da suka nuna.
'Abin da ya jawo lalacewar wuta' - TCN
Tun da fari, mun ruwaito cewa kamfanin TCN ya ce layukan samar da wuta na daya da na biyu masu karfin 330kV na Ugwaji-Apir sun samu matsala.
A cewar TCN, wannan matsalar da aka samu ce ta jawo daukewar wutar lantarki a jihohin Arewacin Najeriya amma injiniyoyin kamfanin na aikin gyarawa.
Asali: Legit.ng