Jami'an Tsaro Sun Gano Sabon Bayani kan Ƴan Ta'addar Lakurawa da Ke Addabar Arewa
- Manjo Janar Adamu Laka ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa babu wata babbar barazana duk da bullar kungiyar Lakurawa a Arewa
- Ya bayyana cewa 'yan ta'addar Lakurawa ba su wuce mutum 200 kawai, kuma an yi shirin murkushe su tare da hadin kan NSA
- Manjo Janar Laka ya yi kira ga jama’a da su guji yada labaran karya da kuma bayar da goyon baya ga ayyukan yaki da ta’addanci a kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ko’odinetan cibiyar yaki da ta’addanci ta kasa, Manjo Janar Adamu Laka, ya kwantarwa da ’yan Najeriya hankali kan ayyukan kungiyar Lakurawa a Sokoto.
Ya ce adadin 'yan kungiyar bai wuce mutum 200 ba, kuma an fara daukar matakan murkushe su tare da hadin gwiwar NSA Mallam Nuhu Ribadu.
Manjo Janar Laka ya yi nuni da cewa, an hada kai da hukumomin tsaro domin tabbatar da rushe kungiyar baki daya, a cewar rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnati za ta murkushe Lakurawa
Duk da sababbin dabarun da Lakurawa ke amfani da su don tayar da hankula, Manjo Janar Laka ya tabbatar da murkushe su idan jama’a sun bada hadin kai.
Da farko kungiyar ta Lakurawa ta fara ayyukan ne da sunan taimakawa jama’a kan ’yan bindiga, amma daga baya ta kafa haraji da iko.
PM News ta rahoto Manjo Janar Laka ya jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu saboda ayyukan kungiyar, yana mai cewa gwamnati ba za ta yarda da wannan ba.
Gwamnati ta tsaurara matakan tsaro
Ya yi bayani kan tsarin tsaro na zamani, cikinsu harda amfani da fasaha domin lura da al’amuran tsaro a iyakokin Najeriya.
Jagoran ya ce an kara tsaurara matakan sa ido kan filayen jiragen sama da iyakoki domin tabbatar da kariya daga duk wata barazana.
Manjo Janar Laka ya bukaci jama’a da su kasance cikin shiri, su guji yada bayanan da ba a tabbatar ba, su kuma tallafawa shirye-shiryen zaman lafiya.
Sojoji sun kaddamar da hari kan Lakurawa
A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar sojin Najeriya ta kai zafafan hare hare kan Lakurawa da suka fara ta'addanci a Arewa ta Yamma.
Gwamnatin jihar Kebbi ta tabbatar da cewa bayan sakin wuta kan miyagun, sun tsere sun bar wasu kayayyaki wadanda sojojin suka kwashe.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng