FCDA: Ministan Tinubu Ya Runtuma Kora a Ma'aikatar Raya Abuja, Bayanai Sun Fito

FCDA: Ministan Tinubu Ya Runtuma Kora a Ma'aikatar Raya Abuja, Bayanai Sun Fito

  • Ministan birnin tarayya, Nyesom Wike, ya dakatar da Hadi Ahmad, shugaban hukumar raya Abuja, dakatarwa ta dindindin
  • A wata sanarwa aka ya fitar a daren Alhamis, an umurci Ahmad da ya mika mulki ga daraktan sashen injiniyanci na hukumar
  • An ce Wike ya yanke wannan hukunci ne saboda wasu abubuwa da ke faruwa a hukumar, kuma ya sha alwashin daidaita lamura

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya dakatar da shugaban hukumar raya birnin tarayya (FCDA), Injiniya Shehu Hadi Ahmad.

Wata sanarwa da aka fitar daren ranar Alhamis ta ce Nyesom Wike ya dakatar da Injiniya Shehu nan take, kuma dakatarwar ta dindindin.

Wike ya fitar da sanarwar dakatar da shugaban hukumar raya birnin tarayya Abuja
Ministan Abuja, Wike ya dakatar da shugaban hukumar raya birnin tarayya. Hoto: @GovWike
Asali: Twitter

Minista ya dakatar da shugaban hukumar FCDA

Lere Olayinka, mai ba Wike shawara kan watsa labarai ne ya fitar da sanarwar wannan matakin, a cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

EFCC: 'Yadda wani gwamna a Najeriya ya tura miliyoyin Naira zuwa asusun ɗan canji'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakatarwar Injiniya Hadi Ahmad wanda ta fara aiki nan take, na daga yunkurin Wike na kawo sabon canji a tsarin shugabancin birnin tarayyar.

Laadership ta rahoto sanarwar ta ce an umarci Injiniya Ahmad da ya mika shugabanci ga daraktan sashen injiniyanci na hukumar FCDA, kamar yadda ake a tsari.

Wike na canje canje a gwamnatin Abuja

Wannan sabon mataki ya biyo bayan wasu canje-canje da suka hada da korar wasu shugabanni da Wike ya yi, da nufin daidaita gudanarwar gwamnatin Abuja.

Ministan na Abuja bai bayyana a fili dalilan dakatarwar da ya yiwa Injiniya Ahmad ba, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin masu sa ido da jami'an gwamnati.

Wannan mataki na Nyesom Wike yana nuni da yadda yake son tabbatar da inganci a cikin harkokin gwamnatin Abuja, inda ya sha alwashin daidaita lamura.

Wike ya ba hukumar FCDA wa'adi

A wani labarin, mun ruwaito cewa minsitan Abuja, Nyesom Wike ya ba shugaban hukumar FCDA wa’adin awa 24 ya yi bayani kan takaddamar babban masallacin Abuja.

Kara karanta wannan

Shugaban NAHCON ya je majalisa, ya tabbatar da zargin da ake tsoro a aikin hajji

A yayin da Wike ya bukaci sanin wurin da masallacin ya ke da kuma tsarin kudin diyya da za a biya, ministan ya kuma karyata masu jita-jitar cewa ya na adawa da Musulunci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.