"Mun Bar Shi da Halinsa:" Gwamnatin Tinubu za Ta Daina Tankawa Atiku

"Mun Bar Shi da Halinsa:" Gwamnatin Tinubu za Ta Daina Tankawa Atiku

  • Fadar shugaban kasa ta ce daga yanzu za ta daina musayar yawu da tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar
  • Gwamnatin ta bayyana cewa akwai manyan ayyuka a gabanta da suka hada raya kasa da farfado da tattalin arziki
  • Hadimin shugaban kasa, Sunday Dare ya ce Bola Ahmed Tinubu zabin yan Najeriya ne , kuma yanzu su ne a gabansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Fadar shugaban kasa ta ce za ta daina musayar yawu da tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Gwamnati ta fadi haka ne a matsayin martani kan shawarar Atiku ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu kan kar ya sake neman kujerar shugabancin Najeriya.

Atiku
Gwamnati za ta daina mayarwa Atiku martani Hoto: Atiku Abubakar/Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa wannan na kunshe a sanarwar mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin sadarwa da wayar da kai, Sunday Dare.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi yadda gwamnati ta tunkari matsalar tattalin arziki gaba gadi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Tinubu za ta daina kula Atiku

Hadimin shugaba Bola Tinubu, Sunday Dare ya bayyana cewa gwamnati ta na da abin yi da ya fi mayarwa Atiku Martani.

Ya fadi haka ne a matsayin martani da ya ce daga yanzu sun daina ba wa tsohon mataimakin shugaban kasar nan saboda muhimmancin kula da Najeriya.

"Jama'a ne gabanmu:" Tinubu ga Atiku

Fadar shugaban kasar nan ta bayyana cewa yan Najeriya sun zabi Tinubu domin aiwatar masu da ayyuka masu ma'ana da za su inganta rayuwarsu.

"“Kasar nan ce a gabanmu, mun gama da Atiku. Ƴan Najeriya ne suka zabi shugaba Bola Tinubu domin ya tafiyar da kasa kuma shi ne abin da aka fi mayar da hankali a kai a yanzu," cewar sanarwar Sunday Dare.

Atiku ya caccaki Tinubu

A baya kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya zargi manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da kara ta'azzara matsalolin da jama'a ke ciki.

Ya bayyana haka a sanarwar da hadiminsa ya fitar, inda ya shawarci gwamnati ta duba sahihan hanyoyin warware matsalolin tattalin arziki domin samar da cigaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.