Za a Rage Zama a Duhu, TCN Ya Ƙara Hasken Wutar Lantarki a Jihohin Arewa 4

Za a Rage Zama a Duhu, TCN Ya Ƙara Hasken Wutar Lantarki a Jihohin Arewa 4

  • Kamfanin TCN na kasa ya bayyana cewa ya kara yawan hasken wutar lantarki da ya ke aikawa wasu jihohin Najeriya
  • Jihohin Arewacin kasar nan guda hudu ne su ka shiga cikin shirin, har da Kano, Kaduna da karin wasu jihohi biyu a shiyyar
  • Kamfanin ya sanar da cewa ya kara yawan hasken wutar da ake ba kamfanoni rarraba hasken wuta (DisCos) a jihohin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na kasa (TCN) ya bayyana shirinsa na kara wadata Arewacin Najeriya da hasken wutar lantarki.

Kamfanin ya dauki sabon matakin bayan matsalolin rashin hasken wuta a shiyyar da ya jawo asarar akalla N1.5bn a kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Wutar lantarki: Asirin yan kwangila ya tonu, EFCC ta zarge su da jawo matsala

Haske
TCN ya kara yawan hasken wutar lantarki ga wasu jihohi Hoto: Transmission Company of Nigeria
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa daraktar yada labaran kamfanin, Ndidi Mbah ta sanar da cewa jihohin Arewa hudu ne za su samu karin hasken wutar lantarki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jihohin da TCN ya karawa hasken lantarki

Kamfanin TCN ya bayyana cewa ya kara yawan hasken wutar lantarki da ya ke turawa kamfanonin rarrabe wuta (DisCos) da ke wasu jihohi hudu.

Daraktar yada labaran kamfanin, Ndidi Mbah ta ce jihohin da su ka yi dacen samun karin hasken wutar sun hada da Jos, Kaduna, Kano, da Yola.

TCN zai rage duhu a wasu jihohin Arewa

TCN ta bayyana abin da zai faru da jihohi hudu da kamfanonin da ke kai masu hasken wutar lantarki su ka samu karin lodi daga babban kamfanin na kasa

Wannan ya na nufin mazauna jihohin za su samu karuwar hasken wutar lantarki a lokacin da ake fatan farfadowa daga tsananin rashin hasken wuta a shiyyar.

Kara karanta wannan

EFCC ta gano abubuwa 3 da suka jawo wutar lantarkin Najeriya ke yawan lalacewa

Kamfanin TCN ya fadi matsalar wutar lantarki

A baya kun ji cewa kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na kasa ya bayyanawa yan Najeriya cewa za su kwana biyu kafin hasken wuta ya dawo yadda ya ke.

Layukan wuta sun kara lalacewa a ranar Alhamis, amma kamfanin TCN ya bayyana cewa tuni ya aika injiniyoyi domin gyara matsalar da aka samu a kuma dawo da haske.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.