Arzikin Najeriya zai Karu, Ana Samar da Gangar Fetur Miliyan 1.8 a Kullum
- Kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya bayyana cewa an samu karuwar danyen fetur da Najeriya ke samarwa kullum
- Shugaban kamfanin NNPCL na kasa, Mele Kyari da ya bayyana haka ya ce ana sa ran adadin zai karu kafin karshen shekara
- Wannan na zuwa ne a bayan NNPCL ya musanta zargin bakin ciki da samuwar matatar fetur ta Dangote a Legas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya ce Najeriya na samar da gangar danyen man fetur sama da ganga 1.8 a kullum.
Kamfanin ya ce an hada hannu da wasu masu ruwa da tsaki ne wajen ƙara yawan gangar fetur da ake fitarwa a kasar.
Jaridar Punch ta a wallafa cewa shugaban kamfanin NNPCL na kasa, Mele Kyari ne ya bayyana cigaban da aka samu a Abuja, inda ya ce za a wuce haka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Najeriya ta kara yawan danyen fetur
Jaridar This day ta wallafa cewa kamfanin mai na kasa ya ce ya kara yawan danyen man fetur da ake samarwa a Najeriya.
Kamfanin NNPCL ya bayyana cewa miliyoyin danyen fetur din da ake fitarwa ya zo daidai da tsarin gwamnatin tarayya ga bangaren mai a kasar.
Kudin shiga ta bangaren fetur zai karu
Ana sa ran karin fitar da danyen fetur da kamfanin NNPCL ya yi zai habaka kudin shiga da gwamnatin tarayya ke samu a bangaren.
Shugaban NNPCL, Mele Kyari ya kara da cewa muradinsa na cewa ana sa ran fara fitar da danyen man fetur ganga miliyan 2 a kullum kafin karshen shekara.
NNPCL ya magantu kan shigo da fetur
A wani labarin kun ji cewa shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Mele Kyari ya ce an daina shigo da fetur daga kasashen waje domin sayarwa a gida Najeriya.
Ya kuma yi bayani kan zargin da ake yi na cewa NNPCL ya na adawa da samuwar matatar mai ta Dangote da aka rika tunanin za ta taimaka wajen saukaka farashin fetur.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng